Connect with us

Labarai

Gwamnatin Kebbi Ta Yaba Wa Sojoji Kan Kafa Sabbin Rundunoni Uku

Published

on

Daga Sani Haruna Dutsin-ma/ B/Kebbi

Gwamnatin Jihar Kebbi ta ce matakin da Hedikwatar Rundunar Sojin Najeriya ta ɗauka na ƙarfafa kasancewar sojoji a jihar, ta hanyar kafa da kuma fara aiki da rundunonin soji guda uku masu muhimmanci, abin farin ciki ne kuma abin maraba.

Kwamishinan Yaɗa Labarai da Al’adu na jihar, Yakubu Ahmed BK, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a Kebbi, inda ya ce wannan mataki ya nuna ƙudirin Rundunar Sojin Najeriya na tunkarar matsalolin tsaro da ke addabar Jihar Kebbi musamman da kuma ƙasar baki ɗaya.

Ya bayyana kafa Brigade mai lamba 28 da Garrison a Birnin Kebbi a matsayin wani muhimmin mataki na ƙarfafa ayyukan tsaro da inganta ƙarfin gudanar da ayyukan soji da kuma tabbatar da ɗaukar matakin gaggawa kan barazanar tsaro da ka iya tasowa, ba a Jihar Kebbi kaɗai ba, har ma da yankunan da ke makwabtaka da ita na jihohin da ke kusa.

Ahmed BK ya kuma yaba wa gudummawar da sauran hukumomin tsaro ke bayarwa, ciki har da Rundunar ’Yan Sandan Najeriya da Hukumar DSS da Hukumar Tsaron Fararen Hula ta Najeriya (NSCDC) da mafarauta da sauran ƙungiyoyin sa-kai na al’umma, wajen haɗa ƙarfi don kare rayuka da dukiyoyin jama’a a faɗin jihar.

Ya ce baya ga Hedikwatar Brigade da ke Birnin Kebbi, fara aiki da Bataliyar Tankoki mai lamba 281 a Yauri da kuma Makaman Atillari a Kaoje, zai ƙara ƙarfafa da kuma daidaita ayyukan yaƙi da ’yan ta’adda da sauran ayyukan soji a faɗin jihar.

A cewarsa, sabbin matakan da aka ɗauka na ƙarfafa ayyukan tsaro sun samo asali ne daga ƙoƙarin da Gwamna Nasir Idris ke yi ba tare da gajiyawa ba, da kuma dagewarsa wajen neman ƙarin tura jami’an tsaro, tare da samar da isassun ma’aikata, kayan aiki da makamai domin tunkarar matsalolin tsaro na musamman da ke fuskantar jihar, waɗanda kuma suke ci gaba da sauyawa.

Ya tabbatar da cewa Gwamnatin Jihar Kebbi za ta ci gaba da bai wa dukkan hukumomin tsaro da ke gudanar da ayyukansu a jihar goyon baya da haɗin kai da ya dace, domin su sauke nauyin da kundin tsarin mulki ya ɗora musu na kare rayuka da dukiyoyi da kuma yaƙi da aikata laifuka.

Alhaji Yakubu Ahmed ya yaba wa Gwamna Nasir Idris bisa salon shugabancinsa mai sauraron jama’a da kuma mai mayar da hankali kan samar da sakamako, wanda ya ce ya taka muhimmiyar rawa wajen ci gaban da ake samu a sassa daban-daban na jihar.

Kwamishinan ya yi kira ga al’ummar Jihar Kebbi da su ci gaba da ba hukumomin tsaro cikakken haɗin kai, ta hanyar gaggauta kai musu sahihan bayanai masu amfani game da ayyuka, wuraren da suke da kuma zirga-zirgar ’yan bindiga, ’yan tada ƙayar baya da sauran masu aikata laifuka.

Fassara: Shafii Abubakar Wababe

Labarai

Ilimi1 day ago

KANO: Ungogo Ta Ƙaddamar da Shirin Shigar da Yara Makaranta

Daga Khadijah Aliyu Ƙaramar Hukumar Ungogo ta Jihar Kano ta ƙaddamar da wani shirin wayar da kan jama’a domin shigar...

Labarai1 day ago

Jihar Naija Ta Dauki Matakan Gaggawa Sakamakon Bullar Cutar Ebola A Abuja

Daga Aliyu Lawal Ma’aikatar Lafiya ta Jihar Nijar ta sanya Cibiyar Ayyukan Gaggawa ta Lafiyar Jama’a (PHEOC) cikin shirin ko-ta-kwana,...

Labarai2 days ago

Gwamnatin Tarayya Ta Ɗauki Matakan Gaggawa Bayan Tabbatar da Ebola a Birnin Tarayya

Daga Bello Wakili  Gwamnatin Tarayya ta fara aiwatar da matakan gaggawa na kare lafiyar jama’a,  bayan tabbatar da bullar cutar...

Labarai2 days ago

Gwamnatin Jigawa Ta Amince Da Fitar Da Naira Biliyan 1.4 Ga Mazabu

Daga Usman Muhammad  Gwamnatin Jihar Jigawa ta amince da kashe sama da naira biliyan 1.4 wajen aiwatar da ayyukan mazabu...

Fasaha2 days ago

Jigawa Ta Ware Naira Miliyan 380 Don Samar da Wutar Lantarki a Cibiyoyin ICT

Daga Usman Muhammad Zaria  Majalisar Zartarwa ta Jihar Jigawa ta amince da kashe sama da naira miliyan 380 wajen samarwa...

Labarai2 days ago

’Yan Sanda Sun Kama Wanda Ake Zargi da Fashi da Makami A Kano

Daga ABDULLAHI JALALUDDEEN, KANO Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano ta kama wani mutum da ake zargi da aikata fashi da...

Labarai2 days ago

2027: Ombugadu Ya Yi Alƙawarin kawo Ƙarshen Rashin Tsaro

Daga ALIYU MURAKI, LAFIA Ɗan takara a zaɓen gwamnan Jihar Nasarawa na jam’iyyar PDP, Dr. Emmanuel Ombugadu, ya yi alƙawarin...

Labarai2 days ago

Tajudeen Zai Bayyana Rahoton Ayyukan Tinubu Cikin Kwanaki 14

Daga BELLO WAKILI, Abuja Shugaban Majalisar Wakilai ta Najeriya, Dr. Abbas Tajudeen, ya ce zai bayyana cikakken rahoton nasarorin da...

Labarai2 days ago

Gwamnatin Zamfara Ta Nuna Damuwa Kan Ƙaruwar Hare-Haren ’Yan Bindiga

Daga AMINU DALHATU Gwamnatin Jihar Zamfara ta bayyana matuƙar damuwarta kan ƙaruwar hare-haren ’yan bindiga a wasu sassan jihar a...

Kasuwanci2 days ago

APC Ta Ce Kebbi Na Tare da Tinubu Dari-bisa-Dari

Daga SANI DUTSINMA Babban Daraktan Yaƙin Neman Zaɓen ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar APC, Sanata Abdulazeez Yari, ya ce...

Mafi Shahara