Connect with us

Labarai

Gwamnan Taraba Ya Yi Ta’aziya Ga Gwamnatin Jihar Neja

Published

on

Daga Aliyu Lawal, Minna

Gwamnan Jihar Taraba, Agbu Kefas, ya jajanta wa Gwamnan Jihar Neja, Mohammed Umar Bago, da al’ummar jihar kan rasuwar masu haƙar ma’adinai 37 da suka mutu a jihar.

Mista Kefas, wanda ya jagoranci tawagar gwamnatin jihar zuwa Gidan Gwamnatin Jihar Neja da ke Minna, ya ce al’ummar Taraba suna jajanta wa iyalan waɗanda suka rasu a wannan lamari, tare da bayyana cewa suna tare da su cikin wannan babban alhini.

Gwamnan Jihar Taraba ya kuma yi amfani da wannan dama wajen yaba wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu bisa kafa kwamitin bincike domin gudanar da bincike kan lamarin. Ya jaddada cewa iyalan waɗanda abin ya shafa na da haƙƙin samun cikakken bayani kan abin da ya faru, kuma sakamakon binciken ya kamata ya haifar da adalci tare da samar da matakan da za su kare rayukan jama’a.

Sai dai ya bayyana fatansa na cewa shugaban kwamitin zai gudanar da aikin yadda ya kamata, la’akari da irin ƙwarewar da yake da ita a fannin tsaro, yana mai cewa yana da yakinin kwamitin zai gabatar da sahihin rahoto.

A nasa jawabin, Gwamnan Jihar Neja, Umar Bago, ya gode wa Gwamnan Taraba da al’ummar jihar bisa kalaman ta’aziyya da suka zo da su a lokacin da jihar ke fuskantar wannan jarrabawa.

Ya ce ziyarar ta nuna kyakkyawan shugabanci, karamci da kuma amincewar da takwaransa na Taraba yake da ita ga gwamnatin Jihar Neja.

Gwamna Bago ya bayyana fatansa na cewa, bisa la’akari da ƙwarewa da kuma mutuncin mutanen da aka zaɓa cikin kwamitin bincike mai zaman kansa, za su gudanar da kyakkyawan aiki. Ya ƙara da cewa kwamitin binciken shari’a da Gwamnatin Jihar Neja ta kafa shi ma yana gudanar da cikakken bincike, kuma yana da yakinin cewa rahotonsa zai ƙara taimakawa wajen cike gibin rahoton kwamitin da Gwamnatin Tarayya ta kafa.

Fassara: Shafii Abubakar Wabbabe

Labarai

Ilimi1 day ago

KANO: Ungogo Ta Ƙaddamar da Shirin Shigar da Yara Makaranta

Daga Khadijah Aliyu Ƙaramar Hukumar Ungogo ta Jihar Kano ta ƙaddamar da wani shirin wayar da kan jama’a domin shigar...

Labarai1 day ago

Jihar Naija Ta Dauki Matakan Gaggawa Sakamakon Bullar Cutar Ebola A Abuja

Daga Aliyu Lawal Ma’aikatar Lafiya ta Jihar Nijar ta sanya Cibiyar Ayyukan Gaggawa ta Lafiyar Jama’a (PHEOC) cikin shirin ko-ta-kwana,...

Labarai2 days ago

Gwamnatin Tarayya Ta Ɗauki Matakan Gaggawa Bayan Tabbatar da Ebola a Birnin Tarayya

Daga Bello Wakili  Gwamnatin Tarayya ta fara aiwatar da matakan gaggawa na kare lafiyar jama’a,  bayan tabbatar da bullar cutar...

Labarai2 days ago

Gwamnatin Jigawa Ta Amince Da Fitar Da Naira Biliyan 1.4 Ga Mazabu

Daga Usman Muhammad  Gwamnatin Jihar Jigawa ta amince da kashe sama da naira biliyan 1.4 wajen aiwatar da ayyukan mazabu...

Fasaha2 days ago

Jigawa Ta Ware Naira Miliyan 380 Don Samar da Wutar Lantarki a Cibiyoyin ICT

Daga Usman Muhammad Zaria  Majalisar Zartarwa ta Jihar Jigawa ta amince da kashe sama da naira miliyan 380 wajen samarwa...

Labarai2 days ago

’Yan Sanda Sun Kama Wanda Ake Zargi da Fashi da Makami A Kano

Daga ABDULLAHI JALALUDDEEN, KANO Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano ta kama wani mutum da ake zargi da aikata fashi da...

Labarai2 days ago

2027: Ombugadu Ya Yi Alƙawarin kawo Ƙarshen Rashin Tsaro

Daga ALIYU MURAKI, LAFIA Ɗan takara a zaɓen gwamnan Jihar Nasarawa na jam’iyyar PDP, Dr. Emmanuel Ombugadu, ya yi alƙawarin...

Labarai2 days ago

Tajudeen Zai Bayyana Rahoton Ayyukan Tinubu Cikin Kwanaki 14

Daga BELLO WAKILI, Abuja Shugaban Majalisar Wakilai ta Najeriya, Dr. Abbas Tajudeen, ya ce zai bayyana cikakken rahoton nasarorin da...

Labarai2 days ago

Gwamnatin Zamfara Ta Nuna Damuwa Kan Ƙaruwar Hare-Haren ’Yan Bindiga

Daga AMINU DALHATU Gwamnatin Jihar Zamfara ta bayyana matuƙar damuwarta kan ƙaruwar hare-haren ’yan bindiga a wasu sassan jihar a...

Kasuwanci2 days ago

APC Ta Ce Kebbi Na Tare da Tinubu Dari-bisa-Dari

Daga SANI DUTSINMA Babban Daraktan Yaƙin Neman Zaɓen ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar APC, Sanata Abdulazeez Yari, ya ce...

Mafi Shahara