Labarai
Jam’iyar PDP ta Rasa Magoya Bayanta A Jihar Kwara
Daga Ali Muhammad Rabi’u, Ilorin
Jam’iyyar PDP reshen Jihar Kwara ta rasa wasu daga cikin mambobinta a Alapa/Onire/Odegiwa Ward da ke ƙaramar hukumar Asa, waɗanda suka sauya sheka zuwa jam’iyyar APC mai mulki.
An karɓi ’yan jam’iyyar da suka sauya shekar ne a yayin taron jam’iyyar na mazabar, wanda Shugaban Hukumar Raya Kogin Ƙananan Neja, LNRBDA, Alhaji Abdullateef Alakawa, da mamba a Majalisar Dokokin Jihar Kwara, Honarabul Rukayat Shittu, tare da shugabannin jam’iyyar da sauran masu ruwa da tsaki suka halarta.
A cewar ’yan jam’iyyar da suka sauya shekar, sun fice daga PDP da ke ƙarƙashin jagorancin Dakta Bukola Saraki ne saboda abin da suka bayyana a matsayin rashin kyakkyawar mu’amala da mambobi da tilasta ɗora wasu mutane kan mukamai da kuma rashin tsarin bai wa mambobi damar cin moriyar jam’iyyar.
Sun ce sun koma APC ne saboda abin da suka bayyana a matsayin ayyukan da ake iya gani da kuma samun damammaki masu kyau ga mambobin jam’iyyar, musamman matasa.
Da yake jawabi a wajen tarbar sabbin mambobin, Alhaji Alakawa ya yi maraba da ’yan siyasar da suka sauya sheka zuwa APC, yana mai cewa babu wani sabon shiga a jam’iyyar, domin kowa ɗaya ne kuma suna aiki tare domin cimma buri guda.
Ya jaddada cewa mutanen da suka yi ƙoƙari kuma suka samu mukaman siyasa suna daga cikin shugabannin jam’iyyar.
Shugaban Hukumar Raya Kogin Ƙananan Neja ya ƙara da cewa Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq ya yi abin a yaba wa al’ummar Asa, yana mai cewa hanya mafi dacewa ta nuna godiya ga ƙoƙarinsa ita ce a mara masa baya tare da zaɓensa a zaɓen Sanatan Mazabar Kwara ta Tsakiya mai zuwa.
Fassara: Shafii Abubakar Wababe
-
Labarai4 days agoHukumar Alhazai Ta Jigawa Ta Bayyana Alhininta Bisa Rasuwar Suleiman Usman
-
Fasaha3 days agoNASENI Ta Ƙarfafa Horar da Sana’o’i da Fasahar Jiragen Sama Marasa Matuki a Kaduna
-
Labarai3 days agoNSCDC Ta Kama Wanda Ake Zargi Da Safarar Mutane A Zamfara
-
Labarai2 days agoGwamnatin Tarayya Ta Ɗauki Matakan Gaggawa Bayan Tabbatar da Ebola a Birnin Tarayya
-
Labarai2 days agoGwamna Uba Sani Ya Ce Bunƙasa Ƙwarewa Na Da Muhimmanci Ga Farfaɗo Da Tattalin Arziki
-
Labarai2 days agoGwamnatin Zamfara Ta Nuna Damuwa Kan Ƙaruwar Hare-Haren ’Yan Bindiga
-
Labarai2 days agoTajudeen Zai Bayyana Rahoton Ayyukan Tinubu Cikin Kwanaki 14
-
Labarai2 days ago’Yan Sanda Sun Kama Wanda Ake Zargi da Fashi da Makami A Kano
