Fasaha
Malaman Makarantun Firamare 1,800 Sun Samu Horo Aka A Kwara
Akalla malaman makarantun firamare 1,800, a fadin kananan hukumomi goma sha shida na jihar Kwara, aaka horar da su kan kara kuzari kan ilimin zamani, hanyoyin amfani da kayan zamani wajen koyarwa.
Da yake bayyana taron bitar na kwanaki goma da aka bude a makarantar sakandire ta Queen Elizabeth da ke Ilorin wanda KwaraLEARN tare da hadin gwiwar hukumar kula da ilimin bai daya ta jihar Kwara (KWSUBEB) ta shirya, kwamishinan ilimi da ci gaban bil’adama na jihar, Dokta Lawal Olohungbebe ya ce shirin na daya daga cikin manyan dabarun da jihar ta bullo da shi na bunkasa harkar ilimi domin ya dace da ka’idojin karni na 21.
Ya kuma bukaci malaman da su ci gaba da jajircewa wajen tsara makomar jihar ta hanyar baiwa al’umma da ilimi da kyawawan dabi’u.
Dokta Olohungbebe ya jaddada shirye-shiryen jihar na tallafa wa ingancin malamai ta hanyar ci gaba da horar da su tare da kayan aikin zamani, a matsayin wani bangare na tafiyar da gwamnati daga tsohon tsari zuwa tsarin ilimin dijital ko zamani.
Kwamishinan ya bayyana kwarin gwiwar cewa horon zai yi tasiri sosai a cikin aji.
Ya bukaci mahalarta taron da su yi amfani da ilimin da suka samu domin ci gaban dalibansu da kuma bangaren ilimi gaba daya.
A nasa jawabin Manajan Darakta na KwaraLEARN, Misis Laide Abel, ta taya mahalarta taron murnar samun horon.
Ta kwadaitar da su da su mai da hankali da kuma taka rawar gani a duk tsawon zaman domin samun cikakkiyar fa’ida daga shirin.
COV/ALI MUHAMMAD RABIU
-
Ilimi6 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai7 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai7 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai7 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Labarai7 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
-
Labarai7 days agoMasu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki
-
Labarai5 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
