Labarai
Kwamitin Majalisar Dokokin Jihar Jigawa Na Ci Gaba Da Rangadi Cibiyoyin Ciyar Da Masu Azumi
Kwamatin duba Shirin samar da abincin buda baki na majalisar dokokin jihar Jigawa a shiyyar Dutse, ya yaba da kyakkyawan yanayin kosai da kunu da ake samarwa domin rabawa masu azumi a cibiyar bada abincin ta 2 a mazabar Kiyako ta karamar hukumar Birnin Kudu.
Shugaban Kwamatin kuma mataimakin Shugaban Majalisar, Alhaji Sani Isyaku Abubakar, ya bayyana haka a lokacin rangadin kwamatin.
Ya bayyana bubukatakarin kayan miya wajen dafa shinkafar da ake rabawa masu azumi.
Da ya ke mayar da jawabi, mai samar da abincin buda baki a cibiyar mazabar Kiyako da ke Babaldu, Salisu Sabo, ya ce suna samar da abincin buda baki da ya hada da shinkafa dafa-duka da kunu da kosai, ga masu azumi 300 a kowace rana.
Salisu Sabo ya yabawa Gwamna Umar Namadi bisa bullo da tsarin ciyar da masu azumi a fadin jihar.
Kwamatin ya Kai makamanciyar wannan ziyara garuruwan Wurno da Kiyako da kuma Birnin kudu.
Kazalika, ya ja hankalin mai aikin dafa abincin buda Baki a cibiyar Gantsa Yamma ya kara kayan miya da mai wajen dafa shinkafar da ake rabawa jama’a.
Ya yi wannan jan hankali ne lokacin da ya jagoranci ‘yan kwamatin domin duba Shirin Samar da abincin buda baki a karamar hukumar Buji, inda ya bukaci masu aikin raba abincin su rinka amfani da safar hannu domin tabbatar da tsafta.
Alhaji Sani Isayku Abubakar ya ce kwamatin yana rangadi ne domin tabbatar da ganin cewa masu aikin dafa abincin su na aiki da tsarin gwamnatin jihar Jigawan wajen dafa abincin da rabawa ga jama’a.
Sai dai kuma, ya yabawa mai aikin dafa abincin a Gantsa bakin Tasha bisa gudanar da aikinsa kamar yadda gwamnati ta bada umarni.
Da ya ke mayar da jawabi, mai aikin dafa abincin buda baki a Gantsa bakin Tasha Malam Sani Yusuf, ya ce ana ba su naira dubu 672 duk kwana uku domin dafa shinkafa kwano 10 da kunu na gero kwano 10 da kosai na wake kwano 10.
A nasa bangaren, Jami’in Shirin na karamar hukumar Buji, Malam Tasi’u Ibrahim Gantsa, ya ce an kafa cibiyoyi 20 a fadin karamar hukumar wadda ake bawa naira 672 cikin kwanaki uku domin Samar da shinkafa da kosai da kunu, bisa kudurin gwamnatin jiha na ciyar da jama’a a watan Azumi.
Usman Mohammed Zaria
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
-
Labarai6 days agoMasu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki
