Connect with us

Ilimi

Gwamnatin Jigawa Za Ta Hada Gwiwa Da Jami’ar Azman Don Inganta Ilimi A Jihar

Published

on

Gwamnatin Jihar Jigawa za ta kulla haɗin gwiwa mai muhimmanci da Jami’ar Azman domin faɗaɗa damar ilimi da inganta ci gaban al’ummar jihar.

An bayyana hakan ne lokacin da shugabannin Jami’ar Azman, karkashin jagorancin Shugabar Jami’ar, Farfesa Fatima Batul Mukhtar, suka kai ziyarar ban girma ga Gwamna Umar Namadi a Fadar Gwamnati da ke Dutse.

Wannan haɗin gwiwa yana da nufin tallafawa sabbin hanyoyin koyarwa, da daukar nauyin dalibai a wasu shirye-shirye na musamman, da kuma inganta basirar matasa a muhimman fannoni kamar lissafi da kwamfuta, da kimiyyar bayanai, da sarrafa harkokin jiragen sama, da sauransu.

Yayin da take jawabi, Shugabar Jami’ar ta nuna godiya ga jajircewar gwamnatin jihar wajen bunkasa ilimi, tare da jaddada aniyar jami’ar wajen samar da inganci da kirkire-kirkire.

Ta kuma yi kira ga gwamnatin jihar da ta hada kai da jami’ar wajen shirye-shiryen horar da matasa da ba su takardun shaidar ƙwarewa, musamman a bangaren shirye-shiryen kwamfuta, tare da manyan kamfanoni irin su Cisco, Huawei, da Oracle Academy.

Mai Girma Gwamna, Jami’ar Azman ta riga ta samu ci gaba a shirye-shiryen kwamfuta, domin mun yi rijista da Cisco, Huawei, da Oracle Academy, kuma muna da malamai da ke da takardar shaidar koyarwa daga Huawei. Saboda haka, muna rokon ku da ku duba yiwuwar yin haɗin gwiwa da mu a shirye-shiryen takardun shaidar ƙwarewa a bangaren shirye-shiryen kwamfuta.”

Shugabar Jami’ar ta kuma yaba wa gwamnatin jihar bisa jajircewarta a fannin ilimi, musamman ware kaso 32 bisa dari na kasafin kudin 2024 ga bangaren ilimi da kuma ƙarin naira biliyan uku da aka ƙara wa Hukumar Tallafin Karatu ta Jihar Jigawa.

A nasa martanin, Gwamna Namadi ya nuna matuƙar godiya ga ƙoƙarin Jami’ar Azman tare da yabawa shugabancin Farfesa Fatima Batul Mukhtar.

Gwamnan ya kuma jaddada muhimmancin shirye-shiryen musamman da jami’ar ke bayarwa, tare da tabbatar da cewa gwamnatin jihar tana da shirin daukar nauyin wasu dalibanta domin su yi karantu a bangarorin da babu a sauran makarantu a jihar.

Sabbin kwasa-kwasan da kuka kirkiro suna da kyau, kuma hakan zai jawo hankalin dalibai da malamai zuwa jami’ar.

Wannan na daga cikin dalilan da suka sa na ga babbar dama a wannan jami’a. Kwasa-kwasan da kuka ambata suna da matukar muhimmanci, musamman a yankunan da basu dawannan taarin karatu.

 

Usman Muhammad Zaria

 

 

Labarai

Labarai4 days ago

Gwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, zai halarci zama na 81 na Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya...

Ilimi5 days ago

An Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo

Daga Khadijah Aliyu  Karamar Hukumar Gwarzo ta Jihar Kano ta raba kayan makaranta guda 20,243 ga ɗaliban makarantun firamare daban-daban...

Labarai6 days ago

Gwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnatin Jihar Jigawa ta sake jaddada aniyarta ta ci gaba da aiki kafada da kafada da...

Labarai6 days ago

Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya

Daga Bello Wakili, Abuja Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya dawo Najeriya bayan ya wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a...

Labarai6 days ago

UNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina

Daga Isma’il Adamu, Katsina Asusun Tallafawa Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya, UNICEF, tare da haɗin gwiwar Hukumar Ilimin Firamare ta...

Labarai6 days ago

NSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Hukumar Tsaro Farin kaya ta Najeriya, NSCDC, reshen Jihar Zamfara, ta kama wani mutum mai shekaru...

Labarai6 days ago

Majalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari

Daga KHADIJAH ALIYU, Kano Majalisar Dokokin Jihar Kano ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta tabbatar da kammala aikin...

Labarai6 days ago

Masu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki

Daga ALI MUHAMMAD RABIU Shirin Ƙarfafa Juriya Ga Sauyin Yanayi A Yankunan Busassun yankuna na Jihar Kwara, KWACReSAL, ya fara...

Ilimi7 days ago

Zamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta

Daga Aminu Dalhatu  Hukumar Ilimin Bai-daya ta Jihar Zamfara, ZSUBEB, ta kaddamar da shirin shigar da yara makaranta na shekarar...

Labarai1 week ago

Gwamnan Kebbi Ya Yabi WAMY Kan Jinya Kyauta Ga Marasa Lafiya

Daga Sani Dutsinma Gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris, ya yaba wa Ƙungiyar Matasa Musulmi ta Duniya (WAMY) kan shirya aikin...

Mafi Shahara