Labarai
Hajjin 2025: Rukunin Farko Na Alhazan Jihar Kwara Ya Tashi Zuwa Kasa Mai Tsarki
Rukunin farko na maniyyata dari biyar da sittin (560) daga jihar Kwara tare da jami’an hukumar aikin hajji ta kasa NAHCON su biyu, sun tashi daga Filin Jirgin Sama na na Babatunde Idiagbon da ke Ilori zuwa Saudiyya domin gudanar da aikin hajjin shekarar 2025.
Yayin da yake jawabi ga maniyyatan kafin tafiyarsu, Gwamnan Jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq, ya bukace su da su kasance masu kamun kai da kuma wakiltar jihar da kasa Najeriya.

Gwamna AbdulRazaq, wanda mai ba shi shawara ta musamman, Alhaji Saadu Salaudeen, ya wakilta, ya yi kira ga dukkan maniyyata 2,174 daga jihar da su yi addu’a domin zaman lafiya da hadin kai a jihar da kuma kasa baki daya.
Gwamnan ya kuma gargadi maniyyatan da su nisanci duk wani hali da zai iya bata suna ko kimar jihar da kasar nan, tare da jaddada bukatar zaman lafiya da fahimta a tsakanin maniyyatan.
A jawabansu, Shugaban Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Kwara, Farfesa Mashood Mahmood Jimba, da Amirul-Hajj na bana, Olupo na Ajase-Ipo, Oba Ismail Yahaya Alebiosu, sun shawarci maniyyatan da su kasance masu hali na gari a tsawon lokacin aikin hajji.

Shi ma a jawabinsa, Shugaban Hukumar Jin Dadin Maniyyatan Musulmi ta Jihar Kwara, Alhaji Abdulkadir Abdulsalam, ya bayyana cewa za a yi sahu 4 wajen jigilar jimillar maniyyata dubu biyu da dari daya da saba’in da hudu (2,174) a matsayin wani bangare na shirye-shiryen aikin hajjin bana.
Maniyyatan sun tashi ne a jirgin Max Airline da karfe goma sha biyu da minti arba’in (12:40) na rana, zuwa kasa mai tsarki.
Ali Muhammad Rabi’u
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
