Connect with us

Labarai

Gwamnatin Tarayya Ta Amince Da Gina Asibitin Dabbobi A Jihar Kwara

Published

on

Ministan Ma’aikatar Kula da Kiwon Dabbobi, Alhaji Idi Mukhtar Maiha, ya bayyana cewa Gwamnatin Tarayya ta amince da gina sabon asibitin dabbobi, da cibiyar ajiye dabbobi, tare da samar da allurar rigakafi a Jihar Kwara.

Ministan ya bayyana hakan ne yayin gabatar da sakamakon nazarin taswirar fadin jihar(Geospatial Mapping) da aka gudanar  a Ilori babban birnin Jihar Kwara.

Da yake wakiltar Ministan, Richard Mbaram ya bayyana wannan shiri a matsayin babbar nasara a tarihi wajen samo mafita ta dindindin ga rikicin manoma da makiyaya a ƙasar nan.

Ya ce aikin na daga cikin tsare-tsaren Shirin Sauya Hanyar Kiwo na Kasa (National Livestock Transformation Plan) na tsawon shekaru goma (2019-2028) wanda ya mayar da hankali kan gyara harkar kiwo a Najeriya.

A nasa jawabin, Kwamishinan Ƙasa na L-Press, Dr. Sanusi Abubakar, ya yaba wa Jihar Kwara bisa zuba jari a bangaren ci gaban kiwo.

Ya yi alkawarin ci gaba da bai wa gwamnatin jihar goyon baya domin cimma sabon tsari a harkar kiwo.

Shi ma Gwamnan Jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq, wanda Mai ba shi Shawara na Musamman Alhaji Sa’adu Salahudeen, ya wakilta, ya yaba wa cibiyar cike ta Jami’ar Bayero Kano bisa jajircewa da ƙwarewar da suka nuna a duk tsawon aikin.

Ya yi alkawarin cewa gwamnatin jihar za ta aiwatar da sakamakon binciken ba tare da kaucewa daga abin da aka gano ba.

Gwamna AbdulRazaq ya yi kira ga sarakuna, abokan hulda, hukumomin tsaro da sauran masu ruwa da tsaki da su hada hannu da gwamnati wajen aiwatar da shawarwarin da binciken ya bayar.

Tun da farko a jawabinsa, Darakta a  Cibiyar Harkar Noma ta Jami’ar Bayero da ke Kano, Farfesa Sanusi Muhammed, ya bayyana cewa binciken ya samar da wani dandali mai inganci don tsara ayyuka, kai agaji, da ƙirƙirar manufofi a bangaren kiwo.

Farfesa Muhammed ya yi kira ga gwamnati da ta yi amfani da bayanan taswirar wajen  gyaran ruwan sha na dabbobi da ƙirƙirar tsarin samar da ruwa mai jure canjin yanayi.

 

ALI MUHAMMAD RABIU

 

 

Labarai

Labarai20 hours ago

Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu

Daga Nasir Malali  Dakarun Sashe na biyu na Rundunar Haɗin Gwiwa ta Arewa maso Yamma, Operation FANSAN YAMMA, sun ceto...

Labarai22 hours ago

NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta

Daga Yusuf Zubairu, Kaduna Hukumar Raya Yankin Arewa Maso Yamma ta bayyana dawo da tsaro a matsayin babban fifikonta a...

Labarai5 days ago

Gwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, zai halarci zama na 81 na Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya...

Ilimi6 days ago

An Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo

Daga Khadijah Aliyu  Karamar Hukumar Gwarzo ta Jihar Kano ta raba kayan makaranta guda 20,243 ga ɗaliban makarantun firamare daban-daban...

Labarai1 week ago

Gwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnatin Jihar Jigawa ta sake jaddada aniyarta ta ci gaba da aiki kafada da kafada da...

Labarai1 week ago

Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya

Daga Bello Wakili, Abuja Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya dawo Najeriya bayan ya wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a...

Labarai1 week ago

UNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina

Daga Isma’il Adamu, Katsina Asusun Tallafawa Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya, UNICEF, tare da haɗin gwiwar Hukumar Ilimin Firamare ta...

Labarai1 week ago

NSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Hukumar Tsaro Farin kaya ta Najeriya, NSCDC, reshen Jihar Zamfara, ta kama wani mutum mai shekaru...

Labarai1 week ago

Majalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari

Daga KHADIJAH ALIYU, Kano Majalisar Dokokin Jihar Kano ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta tabbatar da kammala aikin...

Labarai1 week ago

Masu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki

Daga ALI MUHAMMAD RABIU Shirin Ƙarfafa Juriya Ga Sauyin Yanayi A Yankunan Busassun yankuna na Jihar Kwara, KWACReSAL, ya fara...

Mafi Shahara