Labarai
Gwamnatin Kano Ta Karɓi Rahoton Binciken Kwamishinan Sufuri Kan Belin Wanda Ake Zargi Da Safarar Kwayoyi
Gwamnatin Jihar Kano ta karɓi rahoton kwamitin bincike da aka kafa domin bincikar zargin da ake yi wa Kwamishinan Sufuri, Ibrahim Namadi, kan hannu da yake da shi a ceto wani da ake zargi da safarar miyagun kwayoyi, Sulaiman Aminu Danwawu.
Shugaban kwamitin kuma mai bai wa Gwamna Shawara kan Harkokin Shari’a da Tsarin Mulki, Barrister Aminu Hussain, ne ya mika rahoton ga Sakataren Gwamnati na Jiha, Alhaji Umar Farouk Ibrahim.
Barrister Hussain ya bayyana cewa kwamitin ya gudanar da bincike bisa gaskiya da adalci, da kuma bin hujjoji, ba tare da son rai ba.
Ya bayyana cewa an gayyato Kwamishinan Sufuri domin karin bayani, inda ya kuma gabatar da rubutaccen jawabi ga kwamitin.
Sauran da aka tattauna da su sun hada da Abubakar Umar Sharada, Mataimaki na Musamman kan Wayar da Kan Jama’a, da kuma Musa Ado Tsamiya, Mataimaki na Musamman kan magudanan ruwa.
Don tabbatar da ingancin rahoton, kwamitin ya tuntubi hukumomin tsaro da shari’a kamar DSS, NDLEA da Kungiyar Lauyoyi ta Najeriya (NBA). An kuma duba sahihan takardu da suka danganci lamarin tare da sharuddan doka da suka dace.
Barrister Hussain ya yabawa Gwamna Abba Kabir Yusuf bisa kin tsoma baki da ya yi a lokacin gudanar da binciken, yana mai cewa hakan ya nuna irin shugabanci nagari da girmama tsarin doka.
Da yake karɓar rahoton, Sakataren Gwamnati ya nuna godiya kan yadda kwamitin ya gudanar da aikinsa bisa kwazo da kwarewa, duk da matsin lamba daga jama’a.
Ya jinjina musu kan jajircewa da tsayuwa akan gaskiya, tare da tabbatar da cewa za a mika rahoton ga Gwamna domin nazari da daukar matakin da ya dace.
Ya kara da cewa Gwamnatin Kano za ta duba cikakken rahoton tare da daukar matakan da suka dace bisa shawarar da kwamitin ya bayar.
Abdullahi Jalaluddeen
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
