Connect with us

Ilimi

Gwamna AbdulRazaq Ya Amince Da Naira Biliyan 20 Don Gyaran Gine-ginen Makarantu A Kwara

Published

on

Gwamnan Jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq, ya amince da ware Naira Biliyan 20 a karin kasafin kudin da aka yi domin ci gaba da gyaran gine-ginen makarantu a fadin jihar.

A cikin wata sanarwa da Kwamishinan Ilimi na jihar, Dr. Lawal Olohungbebe, ya fitar, ya ce wannan sabon tsarin zai kara karfi wajen cigaban gyaran makarantun gwamnati.

Sanarwar ta bayyana cewa tuni aka fara aikin, inda aka  zayyana yadda gine-ginen za su kasance, kuma sauran abubuwa za su biyo baya da zaran an amince da karin kasafin kudin.

Sanarwar ta kara da cewa wannan ba wani aiki ne mai zaman kansa ba, illa wata sabuwar babbar gudummawa daga gwamnati don kara habaka aikin da take yi tun da farko.

Ta kara da cewa gwamnatin ta gyara sama da ajujuwa 1,254 banda wasu muhimman ayyukan gyara da aka gudanar a wurare daban-daban.

Gwamnatin ta bayyana jin dadinta kan aiwatar da ayyukan gyaran makarantu na SUBEB-UBEC tun daga shekarar 2014.

Sanarwar ta ce wannan sabuwar gudummawar za ta hada da dakunan gwaje-gwaje da wuraren tsafta a makarantun da ke sassa daban-daban na jihar, domin cike gibi tare da kara karfafa ayyukan da SUBEB ke yi.

Duk da irin manyan ayyukan da muka gudanar, muna sane da cewa har yanzu akwai gibin da ake bukatar cikewa, kuma wannan ne dalilin da ya sa Mai Girma Gwamna ya amince da wannan sabon matakin na musamman don rage gibin da ke cikin gine-ginen makarantu,” In ji sanarwar.

 

Ali Muhammad Rabi’u

Labarai

Labarai4 days ago

Gwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, zai halarci zama na 81 na Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya...

Ilimi5 days ago

An Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo

Daga Khadijah Aliyu  Karamar Hukumar Gwarzo ta Jihar Kano ta raba kayan makaranta guda 20,243 ga ɗaliban makarantun firamare daban-daban...

Labarai6 days ago

Gwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnatin Jihar Jigawa ta sake jaddada aniyarta ta ci gaba da aiki kafada da kafada da...

Labarai6 days ago

Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya

Daga Bello Wakili, Abuja Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya dawo Najeriya bayan ya wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a...

Labarai6 days ago

UNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina

Daga Isma’il Adamu, Katsina Asusun Tallafawa Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya, UNICEF, tare da haɗin gwiwar Hukumar Ilimin Firamare ta...

Labarai6 days ago

NSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Hukumar Tsaro Farin kaya ta Najeriya, NSCDC, reshen Jihar Zamfara, ta kama wani mutum mai shekaru...

Labarai6 days ago

Majalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari

Daga KHADIJAH ALIYU, Kano Majalisar Dokokin Jihar Kano ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta tabbatar da kammala aikin...

Labarai6 days ago

Masu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki

Daga ALI MUHAMMAD RABIU Shirin Ƙarfafa Juriya Ga Sauyin Yanayi A Yankunan Busassun yankuna na Jihar Kwara, KWACReSAL, ya fara...

Ilimi7 days ago

Zamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta

Daga Aminu Dalhatu  Hukumar Ilimin Bai-daya ta Jihar Zamfara, ZSUBEB, ta kaddamar da shirin shigar da yara makaranta na shekarar...

Labarai1 week ago

Gwamnan Kebbi Ya Yabi WAMY Kan Jinya Kyauta Ga Marasa Lafiya

Daga Sani Dutsinma Gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris, ya yaba wa Ƙungiyar Matasa Musulmi ta Duniya (WAMY) kan shirya aikin...

Mafi Shahara