Labarai
An Kaddamar Da Shirin Dashen Itatuwan Dabino Miliyan 50 A Jigawa
Hukumar Yaki da Hamada da Sauyin Yanayi ta Kasa ta kammala shirye-shiryen dasa itatuwan dabino miliyan hamsin (50,000,000) a jihohi goma sha ɗaya 11 da ke fama da fari a Najeriya.
Daraktan Hukumar, Alhaji Salihu Abubakar ne ya bayyana hakan a lokacin ƙaddamar da shirin dasa itatuwan dabinon da aka gudanar a Dutse, babban birnin jihar Jigawa.
Ya ce za a dasa itatuwan dabino guda dubu dari biyar (500,000), tare da wasu nau’o’in itatuwa na gida a faɗin jihar Jigawa.
Alhaji Salihu Abubakar ya yi kira ga jama’a da su rungumi al’adar dasawa da kula da itatuwa domin magance matsalolin hamada, zaizauar ƙasa da sauyin yanayi.
A cewarsa, Hukumar tana aiki tukuru a jihohin da ke fama da fari a Najeriya don yaƙi da hamada, farfaɗo da wuraren da suka lalace a sanadiyar girgizar kasa,, da kuma inganta rayuwar al’ummar karkara.
Ya ce bisa shirin dasa itatuwa, da kuma amfani da albarkatun ƙasa ta hanyar haɗin gwiwar al’umma, Hukumar ta dasa miliyoyin itatuwa tare da farfaɗo da wuraren da ke tallafa wa rayuwa a yankunan da fari ke addaba.
Daga ƙarshe, ya nuna jin daɗinsa bisa jajircewar da gwamnatin jihar Jigawa ta nuna wajen karɓar bakuncin wannan biki na shekara-shekara da aka gudanar a Dutse.
Usman Muhammad Zaria
-
Ilimi6 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai5 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
-
Labarai1 day ago
Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu
-
Labarai1 day ago
NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta
