Fasaha
Gwamnatin Kano Ta Dakatar Da Shirin Tsaftar Muhalli Na Wata Wata Saboda Jarrabawar JAMB
A kokarinta na ganin an gudanar da jarrabawar hadin gwiwa ta hukumar shirya jarabawar shiga jami’a ta JAMB, gwamnatin jihar Kano ta dakatar da aikin tsaftar muhalli na watan Afrilun 2025.
An dauki wannan matakin ne bayan nazari da tuntubar masu ruwa da tsaki, a kokarin baiwa daliban jihar Kano damar rubuta jarabawarsu ba tare da wata matsala ba.
A wata sanarwa da Daraktan wayar da kan jama’a na ma’aikatar muhalli da sauyin yanayi, Ismail Garba Gwammaja ya fitar, ya ruwaito kwamishinan yana cewa.
“Dakatar na da nufin hana duk wani cikas da zai iya kawo cikas ga aikin jarrabawar da kuma tabbatar da cewa ‘yan dalibai za su iya zana jarabawarsu ba tare da wani shamaki ba, in ji Kwamishinan.
Kwamishinan Muhalli da Sauyin yanayi, Dr Dahiru M. Hashim, ya tabbatar wa mazauna jihar cewa dakatarwar na wucin gadi ne na wannan watan kawai, kuma za a ci gaba da aikin tsaftar mahalli ga baki daya a wata mai zuwa, Mayu 2025, a jihar.
Kwamishinan, ya yi kira ga mazauna yankin da su ba hukuma hadin kai da fahimtar dalilin da ya sa aka yanke wannan hukunci.
“Mun himmatu wajen tabbatar da tsafta da lafiya, kuma za mu yi aiki tukuru don ganin cewa ayyukan tsaftar muhalli ba su ci karo da wasu muhimman abubuwan da ke faruwa a jihar ba.”
Yayin da yake yabawa mazauna yankin bisa fahimtarsu da hadin kai da gwamnati mai ci, ya bukace su da su daina zubar da shara ba gaira ba dalili.
“kuma muna ba da hadin kai da ma’aikatan tsaftar muhalli don tabbatar da tsafta da lafiya a ko da yaushe, tare da yin addu’ar samun nasara ga daliban da za su zana jarabawar shiga jami’a ta JAMB ta hadin gwiwa.”
KHADIJAH ALIYU
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
