Ilimi
Sama Da Mutane Miliyan 11 Ne Ke Fama Da Ciwon Suga A Najeriya – Farfesa Zubairu Ilyasu
Wani kwararre a fannin lafiya da ke aiki da asibitin koyarwa na Aminu Kano ya ce bisa kididdigar baya-bayan nan sama da mutane miliyan 11 ne ke dauke da ciwon suga a Najeriya, wasu da dama kuma ba a gano su ba.
Farfesa Zuba Ilyasu, ya bayyana hakan ne a lokacin da yake gabatar da jawabi a taron shekara-shekara na kungiyar likitocin endocrinologists of Nigeria (ACEN) karo na 14, wanda ya gudana a Tahir Guest Palace Kano.
Farfesa Ilyasu ya yi nuni da cewar akwai bukatar wayar da kan jama’a game da salon rayuwa da ake bukatar a yi amfani da su wajen magance matsalar ciwon suga da kuma kiba.
Shugaban taron, Emeritus Farfesa Musa Borodo, ya yi tir da tsadar hanyoyin samar da kiwon lafiya a kasar nan, inda ya jaddada bukatar da ake da shi na samar da dabarun rage radadin cututtuka kamar kiba da ciwon suga.
Borodo ya lura cewa taron zai gyara hanyoyin da za a fadakar da jama’a kan salon rayuwa da kuma rigakafin cututtuka.
Shugaban ACEN, Dr. Williams Balogun, ya bayyana bukatar gwamnati da masu ruwa da tsaki su kara saka hannun jari wajen magance matsalolin cututtuka masu yaduwa.
Ya kuma jaddada kudirin kungiyar na samar da dabarun magance matsalar ciwon suga da kiba.
“Wannan taron zai bayyana ra’ayoyi da bincike iri-iri da nufin tabbatar da cewa an magance wadannan illoli na ciwon suga da kiba sosai.” –
Da yake jawabi a lokacin taron Gwamna Abba Kabir wanda kwamishinan lafiya Dr Abubakar Labaran Yusuf ya wakilta ya ce taron ya zo kan lokaci.
Ya ce gwamnatin jihar Kano ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen hada kai da kungiyoyin likitoci kamar ACEN da nufin hada kai don magance ciwon suga da kiba kasancewar su cututuka masu kalubale.
Abba Kabir Yusuf ya yi kira ga mahalarta taron da su fitar da kudurori da za su magance yawaitar cutar siga da kiba.
Taron na da nufin bayyana ra’ayoyi daban-daban da binciken bincike don magance barazanar ciwon sukari da kuma kiba.
Taron ya ja hankalin mahalarta daga dukkan sassan tarayyar.
ABDULLAHI JALALUDDEEN KANO
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
