Ilimi
Gwamnatin Kano Ta Aika Dalibai 588 Zuwa Jihohin Arewa 13 A Karkashin Shirin Musanya
Gwamnatin jihar Kano ta aika dalibai 588 zuwa jihohin Arewa 13 a karkashin shirin musayar dalibai na shekarar 2025/2026.
An kai daliban zuwa jihohinsu da suka hada da Adamawa, Bauchi, Gombe, Jigawa, Katsina, Kebbi, Taraba, da Nasarawa. Bugu da kari, an kai dalibai daga Yobe, Kaduna, Sokoto, Borno, da Kwara lafiya zuwa inda suke, yayin da wasu dalibai 78 kuma za a kwashe su zuwa jihohin Neja da Benue a ranar 30 ga Satumba, 2025.
Kano dai na daya daga cikin jihohin Arewa 19 da ke halartar wannan shiri, wanda aka tsara shi domin inganta hadin kan kasa, hadewa da fahimtar al’adu tsakanin jahohin mambobin kungiyar.
Da yake jawabi ga manema labarai bayan tafiyar da daliban, kwamishinan ilimi, Dakta Ali Haruna Makoda, wanda Daraktan sa ido da tantancewa, Auwal Muhammad Mustapha ya wakilta, ya jaddada kudirin gwamnati na tabbatar da tsaro da walwalar daliban.
“Mai girma Gwamna, yana ba mu dukkan kayan aiki da tallafin kudi don saukaka ayyukanmu da kuma tabbatar da cewa an kai daliban jihohinsu lafiya,” inji shi.
Dakta Makoda ya kuma yabawa iyaye da masu ruwa da tsaki bisa hadin kai da goyon bayan da suke bayarwa wajen ganin shirin ya samu nasara.
COV/Khadija Aliyu
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
