Connect with us

Labarai

Tinubu Ya Jajantawa Iyalai Wadanda Gobara Ta Shafa A FIRS, UBA Da United Capital

Published

on

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana matukar alhininsa kan asarar rayuka da aka yi a gobarar da ta tashi a ranar Talata a Afriland Towers da ke Broad Street, a  Legas.

 

A cikin wata sanarwa da mai baiwa shugaban kasa shawara kan yada labarai, Bayo Onanuga ya fitar, ya ce shugaba Tinubu ya jajantawa iyalan wadanda abin ya shafa, da kuma hukumomi da ma’aikatan hukumar tara haraji ta tarayya (FIRS), United Capital, United Bank for Africa (UBA) Plc, da kuma Afriland Properties Limited.

 

Ya kuma jajanta wa wadanda suka rasa ‘yan uwansu a wannan bala’in, tare da yi wa wadanda suka jikkata fatan samun sauki cikin gaggawa.

 

Shugaba Tinubu ya yaba da matakin da hukumomin gaggawa suka dauka da suka hada da hukumar kashe gobara ta tarayya, da masu bayar da agajin gaggawa, da kungiyoyin likitoci, da sauran jama’a, wadanda suka taimaka wajen kwashe mutanen daga ginin da lamarin ya shafa a kan lokaci.

 

Yayin da yake ba da shawarar yin taka tsantsan, horarwa, da kuma taka tsan-tsan don hana afkuwar irin haka nan gaba, shugaban ya yi addu’ar Allah ya jikan wadanda suka rasu, ya kuma yiwa iyalan wadanda suka rasa rayukansu ta’aziyya.

 

Bello Wakili

Labarai

Labarai1 day ago

Kano: Kotu Ta Umarci A Lalata Buhunan Fulawa Sama Da 400

Daga Khadijah Aliyu  Wata kotu a Jihar Kano ta bayar da umarnin lalata buhunan fulawa sama da 400 da suka...

Labarai2 days ago

Tinubu Ya Jaddada Ƙudurin Samar Da Ci Gaba A Jigawa

Daga Usman Muhammad Zaria  Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya sake jaddada ƙudurin gwamnatinsa na ci gaba da aiwatar da...

Labarai2 days ago

Shugaban Gidan Talabijin Na Katsina Abba Zayyan Ya Yi Murabus

Daga Isma’il Adamu  Babban Manajan gidan talabijin na Jihar Katsina (KTTV), Abba Zayyan, ya miƙa takardar murabus daga muƙaminsa a...

Labarai2 days ago

Namadi Ya Miƙa Buƙatu Uku Ga Tinubu Kan Ci gaban JiharJigawa

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya bukaci Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya kai musu...

Labarai2 days ago

Arewa Za Ta Saka Wa Tinubu Da Ruwan Kuri’a A 2027- Yari

Daga Usman Muhammad Zaria  Daraktan Janar na Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen Shugaban Ƙasa na APC, Sanata Abdulaziz Yari, ya ce...

Labarai2 days ago

Shettima Ya Bukaci ’Yan Najeriya Su Sake Zaben Tinubu A 2027

Daga Usman Muhammad Zaria  Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya bukaci ’yan Najeriya da su goyi bayan sake zaɓen Shugaba...

Labarai3 days ago

Jigawa Ta Amfana Da Ayyukan Gwamnatin Tinubu – Abdulaziz

Daga Usman Muhammad Zaria Babban Mataimaki na Musamman ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu kan harkokin yada labarai da wayar dan...

Labarai3 days ago

Majalisar Kano Za Ta Karɓi Kasafin Kuɗin Shekarar 2027

Daga Khadijah Aliyu  Majalisar Dokokin Jihar Kano na shirin karɓar daftarin kasafin kuɗin shekarar 2027 daga Gwamna Abba Kabir Yusuf...

Labarai4 days ago

Yankin Funtua Sun Yi Fitowar Farin Dango A Yakin Neman Zaɓe Na APC- Hamza Faskari

Daga Isma’il Adamu  An bayyana yakin neman zaben jam’iyyar APC a yankin Sanatan Funtua na Jihar Katsina a matsayin nasara,...

Labarai4 days ago

Namadi Ya Ƙaddamar Da Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen APC Na 2027

Daga Usman Muhammad Zaria Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya ce an haɗa kwamitocin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa...

Mafi Shahara