Kasuwanci
Gwamnatin Jigawa Ta Kaddamar Da Shirin Tallafawa Masu Kanana Da Matsakaitan Sana’o’i
Gwamnatin jihar Jigawa ta kashe sama da naira miliyan dubu dari da sittin da hudu wajen tallafawa kanana da matsakaitan masana’antu a jihar.
Gwamna Umar Namadi ya bayyana hakan a lokacin kaddamar da rabon katin cire kudi na ATM ga wadanda suka ci gajiyar shirin inganta rayuwar al’umma na gwamnatin tarayya da aka gudanar a sakatariyar karamar hukumar Dutse.

Malam Umar Namadi ya bayyana cewar, hukumar bunkasa tattalin arziki ta jihar ce ta fitar da ta hannun shirin farfadowa daga annobar cutar corona.
A cewar sa, kusan mutane dubu ashirin da uku ne za su amfana da tallafin naira dubu saba’in da biyar a jihar.
Yana mai cewar, hakan na daga cikin kudirin shugaban kasa na Renewed Hope agenda na tallafawa masu karamin karfi domin bunkasa tattalin arzikin su.

A don haka, Namadi ya yi kira ga wadanda za su cigajiyar shirin da su yi cikakken amfani da kudaden wajen inganta rayuwar iyalansu.
Wakilinmu ya aiko mana da rahoton cewar, wadanda suka yi jawabai sun hada da mataimakan Gwamnan jihar, Injiniya Aminu Usman da shugaban karamar hukumar Dutse da jami’in kula da shirin inganta rayuwar al’umma na jihar Alhaji Mustapha Umar Babura.
Wasu daga cikin wadanda suka amfana da tallfin sun yabawa Gwamnatin jihar da ta tarayya bisa bullo da shirin.
Usman Mohammed Zaria
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
-
Labarai6 days agoMasu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki
