Labarai
Gwamna Namadi Ya Rantsar da Sabbin Kwamishinonin Hukumar Ma’aikata
Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya rantsar da sabbin kwamishinonin dindindin guda biyu na Hukumar Ma’aikatan Jihar.
Wadanda aka nada su ne Alhaji Babandi Saleh a matsayin Kwamishina na Dindindin na 2 da kuma Alhaji Ibrahim Adamu Fagam a matsayin Kwamishina na Dindindin na 3. An gudanar da bikin rantsuwar ne a zauren majalisar zartaswa na gidan gwamnati da ke Dutse.
Da yake jawabi a wajen taron, Gwamna Namadi ya jaddada kudirin gwamnatinsa na ƙarfafa ma’aikata domin tabbatar da ingantaccen tsarin gudanarwa.

Ya bayyana ma’aikata a matsayin ginshiƙi na aiwatar da manufofi da shirye-shiryen gwamnati, yana mai cewa nadin kwamishinonin dindindin a karon farko wani bangare ne na sabbin sauye-sauyen da ake yi.
Gwamnan ya taya sabbin kwamishinonin murna tare da jan hankalinsu da su yi aiki da gaskiya, ƙwarewa da jajircewa.
Ya nuna kwarin gwiwa cewa sabbin kwamishinonin za su bayar da gudummawa sosai ga cigaban Jihar Jigawa.

Da yake jawabi a madadin wadanda aka nada, Alhaji Babandi Saleh ya gode wa gwamnan bisa amincewa da su, tare da yin alkawarin jajircewa wajen aiwatar da shirin sauye-sauyen gwamnati.
Ya tabbatar da cewa za a samu haɗin kai tsakanin Hukumar Ma’aikata da sauran hukumomi domin kawo canji mai kyau.
Alhaji Saleh ya kuma yi alkawarin cewa kwamishinonin ba za su ci amanar gwamnati da al’umma ba, za su kuma yi aiki tukuru don tabbatar da burin da ake da shi a kansu.
Taron ya samu halartar manyan jami’an gwamnati da masu ruwa da tsaki a harkar ma’aikatan jihar.
Usman Muhammad Zaria
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
-
Labarai6 days agoMasu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki
