Labarai
Builder Uba Ya Taya Sabon Shugaban ALGON Na Jihar Jigawa Murna
Shugaban Karamar Hukumar Birnin Kudu, Dr. Builder Muhammad Uba, ya taya Shugaban Karamar Hukumar Dutse, Dr. Sibu Abdullahi murna, bisa samun nasarar zama sabon Shugaban Ƙungiyar Ƙananan Hukumomin Najeriya (ALGON) a Jihar Jigawa.
A wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata, Dr. Uba ya bayyana zaben Dr. Sibu a matsayin gagarumar nasara tare da yi masa fatan alkhairi yayin aikinsa.
Ya bayyana kwarin gwiwar cewa jagorancin Dr. Sibu zai ƙarfafa haɗin kai da fahimtar juna tsakanin ƙananan hukumomi 27 na jihar, wanda hakan zai haɓaka samar da ci gaba, tare da inganta tattalin arziki a fadin Jigawa.
Dr. Uba ya kuma yi addu’ar fatan alkhairi ga Jihar Jigawa da shugabanninta domin cimma nasarar manufofin da aka sanya a gaba.
Shugaban Karamar Hukumar Birnin Kudu ya yi wa Dr. Sibu fatan samun nasarar shugabanci tare da bayyana tabbacin cewa jagorancinsa zai yi tasiri mai kyau ga al’ummar Jihar Jigawa.
Usman Muhammad Zaria
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
-
Labarai6 days agoMasu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki
-
Labarai4 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
