Kasuwanci
Gwamna Namadi Ya Bayyana Karfafa Matasa A Matsayin Jigon Ayyukan Gwamnatinsa
Gwamna Umar Namadi na jihar Jigawa ya jaddada kudirinsa na karfafawa matasa sana’o’i da ayyukan yi a jihar.
Ya bayyana haka ne a yayin bikin bude wani katafaren shago da wani bawan Allah ya gina a kan titin Malam-Madori a karamar hukumar Hadejia.

Ya bayyana cewa, bai wa matasa damar yin sana’o’i shi ne jigon tsare-tsaren gwamnati mai dauke da manufofi 12, da ke da nufin daukaka jihar zuwa matsayi mafi girma.
A cewarsa, daya daga cikin ginshikan tsare-tsaren gwamnatinsa shi ne samar da damammaki da ke bai wa matasa sana’o’in dogaro da kai, domin samun ci gaba a kasuwar hada-hadar kudi.
Gwamna Namadi ya ce, gwamnatin jihar ta kaddamar da kafa shaguna da za a rika sayar da kayayyaki a farashi mai rahusa a fadin jihar domin amfanin al’umma.
Don haka Gwamnan ya yaba da kafa wannan katafaren shago a garin Hadejia, inda ya bayyana shi a matsayin gudunmawa kuma abin yabawa ga al’umma.

Ya bayyana shi a matsayin wani muhimmin abu da zai samar da ayyukan yi, musamman ga matasa.
Namadi, ya jaddada kudirin gwamnatin jihar na tallafawa daidaikun mutane da ‘yan kasuwa da ke ba da fifiko wajen inganta rayuwar al’umma.
“Za mu ci gaba da karfafa wa wadanda suka nuna kwazo wajen kyautata rayuwar jama’armu da ci gaban al’ummarmu. Inji shi.
Usman Muhammad Zaria
-
Ilimi6 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai5 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
-
Labarai20 hours ago
Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu
-
Labarai22 hours ago
NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta
