Connect with us

Labarai

’Yan Sanda a Zamfara Sun Ceto Mutane 25 Bayan Dakile Harin ’Yan Bindiga a Damba

Published

on

Daga Aminu Dalhatu

Rundunar ’Yan Sanda a Jihar Zamfara ta ce ta samu nasarar ceto mutune 25 da aka yi  yunkurin sacewa, bayan  wani hari da ’yan bindiga suka kai wa kauyen Kuraje da ke yankin Damba a Karamar Hukumar Gusau.

Wata sanarwa da Jami’in Hulda da Jama’a na Rundunar, DSP Yazid Abubakar, ya fitar ta bayyana cewa lamarin ya faru ne a daren Juma’a 21 ga watan Nuwamban 2025, da misalin karfe 10 saura kwara, lokacin da gungun ‘yan bindiga dauke da makamai suka mamaye yankin, suna harbe-harbe tare da tasa keyar  mata 10 da yara 15 domin tafiyada su.

Sanarwar ta ce bayan samun kiran gaggawa, tawagar sintiri ta ’yan sanda daga sashen Damba da Sashen Ayyuka na Gusau tare da hadin guiwar jami’an tsaro na sa kai wato Community Protection Guards (CPG) sun hanzarta isa yankin.

Jami’an sun bi diddigin ’yan bindigar da suka tsere sannan suka shiga wani salon aiki na dabaru wanda ya kai ga kubutar da dukkan mutanen da aka sace.

DSP Abubakar ya ce an garzaya da wadanda aka ceto zuwa Sabongari Damba domin tabbatar da tsaronsu, duba lafiyar su da tantance su kafin a mika su ga iyalansu.

Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Zamfara, CP Ibrahim Balarabe Maikaba, ya jinjinawa jarumta da kwarewar jami’an da suka gudanar da aikin.

Ya kuma tabbatar da kudirin rundunar na ci gaba da kare rayuka da dukiyoyin jama’ar jihar.

 

 

Labarai

Labarai16 hours ago

Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu

Daga Nasir Malali  Dakarun Sashe na biyu na Rundunar Haɗin Gwiwa ta Arewa maso Yamma, Operation FANSAN YAMMA, sun ceto...

Labarai18 hours ago

NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta

Daga Yusuf Zubairu, Kaduna Hukumar Raya Yankin Arewa Maso Yamma ta bayyana dawo da tsaro a matsayin babban fifikonta a...

Labarai5 days ago

Gwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, zai halarci zama na 81 na Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya...

Ilimi6 days ago

An Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo

Daga Khadijah Aliyu  Karamar Hukumar Gwarzo ta Jihar Kano ta raba kayan makaranta guda 20,243 ga ɗaliban makarantun firamare daban-daban...

Labarai7 days ago

Gwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnatin Jihar Jigawa ta sake jaddada aniyarta ta ci gaba da aiki kafada da kafada da...

Labarai7 days ago

Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya

Daga Bello Wakili, Abuja Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya dawo Najeriya bayan ya wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a...

Labarai7 days ago

UNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina

Daga Isma’il Adamu, Katsina Asusun Tallafawa Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya, UNICEF, tare da haɗin gwiwar Hukumar Ilimin Firamare ta...

Labarai7 days ago

NSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Hukumar Tsaro Farin kaya ta Najeriya, NSCDC, reshen Jihar Zamfara, ta kama wani mutum mai shekaru...

Labarai7 days ago

Majalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari

Daga KHADIJAH ALIYU, Kano Majalisar Dokokin Jihar Kano ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta tabbatar da kammala aikin...

Labarai7 days ago

Masu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki

Daga ALI MUHAMMAD RABIU Shirin Ƙarfafa Juriya Ga Sauyin Yanayi A Yankunan Busassun yankuna na Jihar Kwara, KWACReSAL, ya fara...

Mafi Shahara