Labarai
An Kashe Wata Mata Bisa Kuskure A Jihar Kwara.
Wasu fusatattun mutane sun kashe wata mata da aka yi kuskure daukar ta cikin masu garkuwa da mutane ce a babbar kasuwar Ipata da ke karamar hukumar Ilorin ta Gabas a jihar Kwara.
Gidan rediyon Najeriya ya tattaro cewa lamarin ya faru ne da safiyar alhamis, inda aka ga matar wadda daga baya aka gano ashe mai bukata ta musamman ce tana yawo a cikin al’umma.
Da yake tabbatar da lamarin, jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan (PPRO), Toun Ejire-Adeyemi, a wata sanarwa da ya fitar, ya bayyana lamarin a matsayin abin takaici.
“Bayanan sun samu cewa an ga wata mata da ake zargin wacce mai bukata ta musamman ce tana yawo a cikin al’umma, wasu jama’a da ba su sani ba sun yi zargin cewa ita ce mai garkuwa da mutane.
Ya kara da cewa, da gaggawa tawagar ‘yan sanda da ke sintiri suka garzaya wurin da lamarin ya faru, inda suka kubutar da matar da abin ya faru akanta sannan suka garzaya da ita babban asibitin Ilorin domin samun kulawar gaggawa.
Ya ce abin takaici, likitan da ya duba ta ya tabbatar da mutuwar ta sakamakon raunukan da ta samu.
Sanarwar ta ce an ajiye gawarwakinta a dakin ajiyar gawarwaki na asibitin, yayin da aka fara bincike mai zurfi.
ALI MUHAMMAD RABIU
-
Ilimi6 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai5 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
-
Labarai22 hours ago
Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu
-
Labarai1 day ago
NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta
