Kasuwanci
Hukumar Kwastam Ta Kama Kilo 420 Na Bawon Dabbar Dankunya A Kano
Hukumar Kwastam ta Najeriya reshen Kano/Jigawa, ta kama wani adadi mai yawa na bawon dabbar Dankunya wato pangolin mai nauyin kilogiram 420 a wata unguwa da ke cikin birnin Kano.
Shugaban Hukumar Kwastam, Abubakar Dalhat ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Kano.
Ya ce an gudanar da aikin ne a ranar 16 ga Yuli, 2025, sakamakon hadin gwiwa tsakanin jami’an kwastam da sauran hukumomin da abin ya shafa. Abubakar Dalhat ya bayyana cewa, an gudanar da wannan aiki ne da nufin yakar haramtacciyar kasuwancin namun daji da sauran laifukan da suka hada da kare albarkatun kasa da Najeriya ke da kima ga al’umma na yanzu da kuma masu zuwa.
Ya bayyana cewa kama wannan bawondabbar pangolin ba wai kawai yana wakiltar lalata hanyoyin masu laifi ba ne, har ma yana aike da sako mai ƙarfi ga masu fataucin namun daji cewa ba za a amince da aikata laifuka kan namun daji ba a Najeriya ko kuma a duk faɗin duniya.
“Muna ci gaba da jajircewa wajen kare muhallinmu da namun daji kamar yadda sashi na 55 na dokar hukumar kwastam ta Najeriya ta 2023 ta bukata.”
Shugaban Kwastam din ya yabawa Kwanturola Janar na Hukumar Kwastam, Bashir Adewale Adeniyi MFR, bisa jajircewarsa da goyon bayansa wajen gudanar da wannan aiki.
Ya kuma gode wa abokan huldar kasa da kasa, irin su ofishin hulda da kasa da kasa na Yanki da kuma Focus Conservation, saboda taimakon da suke bayarwa.
ABDULLAHI JALALUDDEEN KANO
-
Labarai2 days agoIran ta Tabbatar da Kisan Ayatollah Khamenei a Hare-haren Amurka da Isra’ila
-
Labarai4 days agoMajalisar Dokokin Jihar Kaduna Ta Amince da Kasafin Kudin Kananan Hukumomin Jihar na 2026
-
Labarai4 days agoAzumin Ramadan: Shugaban Karamar Hukumar Birnin Kudu Ya Bada Tallafin Kudi ga Marasa Galihu
-
Labarai6 days agoUwargidan Gwamnan Zamfara Ta Kaddamar da Rabon Tallafin Ramadan ga Marasa Galihu
-
Labarai3 days agoBankin Raya Kasashen Afirka Zai Samar da Shirin Bunƙasa Aikin Noma a Jigawa
-
Labarai6 days agoWani Bam Kirar Hannu Ya Fashe a Kan Hanyar Gusau Zuwa Funtua
-
Labarai3 days agoGwamnatin Jigawa ta Gargadi ‘Yan Kwangila Kan Ingancin Abincin Ramadan
-
Labarai3 days agoMasarautar Hadejia ta Raba Zakkar Kayan Amfanin Gona da Dabbobi a Garin Unik
