Ilimi
Kwara Ta Kafa Tutar Hadin Kai Mai Mita 70 A Ilorin
Gwamnatin jihar Kwara ta kafa tutar hadin kai mai tsayin mita 70 a hukumance, wanda ke zama alamar “hadin kan kasa, tafiya tare da buri a matsayin al’umma”.
Da yake jawabi a wani takaitaccen biki a Ilorin, Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq ya ce jihar ba ta daga tuta kawai ba, a’a tana nuna kwarin guiwar wata alama ce ta hadin kai, alfahari, da kuma kishin kasa.
Gwamnan ya samu wakilcin kwamishinan sadarwa na jihar Bola Olukoju, wanda wasu kwamishinoni uku suka taimaka masa: Aliyu Kora Sabi (sufuri); Nafisat Buge (Muhalli); da Nnafatima Imam (ci gaban al’umma) da sauran manyan baki.
A cewarsa, sandar tuta na kara karfafa martabar jihar a matsayin cibiyar kirkire-kirkire, al’adu, da jagoranci mai ma’ana.
Gwamna Abdulrazaq ya yi bayanin cewa, alamar za ta zama babban abin jan hankali, jawo masu ziyara, da samar da damammaki, da kuma baje kolin dabarun saka hannun jari na jihar kan ababen more rayuwa da ba wai kawai a yi amfani da su ba har ma da karfafa gwiwa.
Ya ce gwamnatinsa ta gina tituna, asibitoci na zamani, da karfafa samar da ruwan sha tare da bayar da tallafi ga manoma, ‘yan kasuwa, da kuma bangarori daban-daban na al’umma.
COV/ALI MUHAMMAD RABIU
-
Ilimi6 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai5 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
-
Labarai20 hours ago
Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu
-
Labarai22 hours ago
NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta
