Labarai
‘Yan Ƙwadago Sun Yi Watsi Da N48,000 A Matsayin Mafi Ƙarancin Albashi
Ƙungiyar Ƙwadago NLC ta yi fatali da tayin naira 48,000 da Gwamnatin Tarayya ta gabatar a matsayin mafi ƙarancin albashin ma’aikata a ƙasar.
Mambobin ƙungiyar ta NLC a wannan Larabar sun bayyana mamakin dalilin da gwamnati da mambobin kamfanoni masu zaman kansu ke tozarta su da abin da ta bayyana a matsayin tayi mai ban dariya.
Radio Nigeria ya ruwaito cewa a yayin da Gwamnatin Tarayya ta miƙa tayin Naira 48,000, ‘yan ƙungiyoyi masu zaman kansu suka miƙa tayin N54,000.
Sai dai ƙungiyar NLCn ta bayyana adawartwa kan duk tayin da ɓangarorin biyu suka gabatar a wani taron tattaunawa da aka gudanar a babban Ofishin NLC na Labour House da ke Abuja.
Shugabannin ƙwadagon sun ce gwamnati ba ta gabatar da wasu bayanai da za su goyi bayan tayin da ta gabatar ba.
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai7 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai7 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Labarai7 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
-
Labarai7 days agoMasu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki
-
Labarai5 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
