Labarai
2027: Ombugadu Ya Yi Alƙawarin kawo Ƙarshen Rashin Tsaro
Daga ALIYU MURAKI, LAFIA
Ɗan takara a zaɓen gwamnan Jihar Nasarawa na jam’iyyar PDP, Dr. Emmanuel Ombugadu, ya yi alƙawarin kawo ƙarshen matsalar rashin tsaro da kuma bai wa bunƙasa ababen more rayuwa fifiko a faɗin jihar, idan aka zaɓe shi a matsayin gwamna a shekarar 2027.
Dr. Emmanuel Ombugadu ya bayyana hakan ne yayin ƙaddamar da rangadin yaƙin neman zaɓen jam’iyyar PDP na babban zaɓen shekarar 2027, wanda aka gudanar a Ƙaramar Hukumar Awe ta jihar.
Ya ce gwamnatinsa za ta bai wa tsaro fifiko, yana mai cewa dole ne al’ummar jihar, waɗanda mafi yawansu manoma ne, su samu damar zuwa gonakinsu, su kwana cikin kwanciyar hankali, tare da gudanar da harkokin rayuwarsu ba tare da fargaba ba.
Ya kuma bayyana cewa gwamnatinsa za ta mayar da hankali wajen bunƙasa ababen more rayuwa, ciki har da ginawa da gyaran hanyoyi domin sake haɗa al’ummomi da bunƙasa harkokin tattalin arziki.
Dr. Emmanuel Ombugadu ya ce gwamnatinsa za ta tabbatar da gina hanyoyin da suka haɗa Akiri da Jihar Filato, da sauran muhimman hanyoyi. Ya kuma yi alƙawarin haɗa jihohin Binuwai da Nasarawa da Taraba da Filato ta hanyoyin da za su sauƙaƙa zirga-zirga da ƙarfafa haɗin kai da bunƙasa kasuwanci.
Da yake nasa jawabin, Shugaban PDP na jihar, Dr. Daniel Gimba, ya ce ƙaddamar da yaƙin neman zaɓen ya nuna aniyar jam’iyyar ta kawo ƙarshen wahalhalu tare da samar da shugaba na gari wanda zai kai jihar ga ci gaba.
Shi ma da yake magana a madadin sauran ’yan takara, ɗan takarar sanatan Nasarawa ta Kudu na PDP, Dr. Mike Omeri, ya nuna godiyarsa ga magoya baya da mambobin jam’iyyar bisa amincewar da suka nuna musu.
A nasa ɓangaren, Mukaddashin Shugaban Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen PDP, Mark Ogbole, ya ce jam’iyyar ta zaɓi fara yaƙin neman zaɓenta na lumana a Awe ne domin isar da saƙonta ga dukkan sassan jihar.
Ya yi alƙawarin cewa gwamnatin PDP za ta samar da ayyukan yi ga matasa tare da tallafa wa mata masu sana’o’i domin inganta rayuwarsu da ta iyalansu. Ya jaddada cewa jam’iyyar na neman mulki ne ba domin ta ci zaɓe ta gudu ba, sai dai domin ta yi aiki wa al’ummar jihar.
Fassara: Shafii Abubakar Wababe
-
Labarai4 days agoHukumar Alhazai Ta Jigawa Ta Bayyana Alhininta Bisa Rasuwar Suleiman Usman
-
Fasaha3 days agoNASENI Ta Ƙarfafa Horar da Sana’o’i da Fasahar Jiragen Sama Marasa Matuki a Kaduna
-
Labarai3 days agoNSCDC Ta Kama Wanda Ake Zargi Da Safarar Mutane A Zamfara
-
Labarai2 days agoGwamna Uba Sani Ya Ce Bunƙasa Ƙwarewa Na Da Muhimmanci Ga Farfaɗo Da Tattalin Arziki
-
Labarai2 days agoGwamnatin Tarayya Ta Ɗauki Matakan Gaggawa Bayan Tabbatar da Ebola a Birnin Tarayya
-
Labarai2 days agoGwamnatin Zamfara Ta Nuna Damuwa Kan Ƙaruwar Hare-Haren ’Yan Bindiga
-
Labarai2 days ago’Yan Sanda Sun Kama Wanda Ake Zargi da Fashi da Makami A Kano
-
Labarai2 days agoTajudeen Zai Bayyana Rahoton Ayyukan Tinubu Cikin Kwanaki 14
