Labarai
Hukumar Alhazai Ta Jigawa Ta Bayyana Alhininta Bisa Rasuwar Suleiman Usman
Daga Usman Muhammad
Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Jigawa ta bayyana rasuwar tsohon shugabanta, Alhaji Suleiman Usman, a matsayin babban rashi ga jihar da Najeriya baki ɗaya.
Darakta Janar na hukumar, Alhaji Ahmed Umar Labbo ne ya bayyana hakan yayin ziyarar ta’aziyya da ya kai wa iyalan marigayin a Jihar Kano.
Labbo, wanda Daraktan Ayyuka na hukumar, Alhaji Muhammad Garba ya wakilta, ya mika sakon ta’aziyyarsa ga iyalan marigayin, abokansa, Hukumar Alhazai ta Ƙasa (NAHCON) da daukacin al’ummar Musulmi bisa wannan rashi.
Ya yaba da irin gudunmawar da marigayi Suleiman Usman ya bayar wajen bunƙasa Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Jigawa, musamman ta fuskar shugabanci, sadaukarwa da ƙoƙarin inganta ayyukan aikin Hajji.
Labbo ya bayyana marigayin a matsayin gogaggen ma’aikacin gwamnati mai mutunci, wanda ya yi wa jihar da ƙasa baki ɗaya hidima cikin gaskiya da riƙon amana.
Ya roƙi Allah Maɗaukakin Sarki da Ya gafarta wa marigayin, sannan Ya ba iyalansa haƙurin jure wannan babban rashi.
Marigayi Alhaji Suleiman Usman, wanda ya fito daga garin Hadejia a Jihar Jigawa, ya kasance ɗaya daga cikin daraktocin farko na jihohi da shiyyoyi a Hukumar Alhazai ta Ƙasa (NAHCON). Ya kuma taɓa riƙe muƙamin Daraktan Tsare-tsare, Bincike, Ƙididdiga, Yaɗa Labarai da Ayyukan Laburare (PRSILS) na hukumar.
Marigayin ya rasu ne a ranar Asabar bayan fama da doguwar jinya, an kuma yi jana’izarsa a Jihar Kano.
Fassara: Safiyah Abdulkadir
-
Fasaha3 days agoNASENI Ta Ƙarfafa Horar da Sana’o’i da Fasahar Jiragen Sama Marasa Matuki a Kaduna
-
Labarai3 days agoNSCDC Ta Kama Wanda Ake Zargi Da Safarar Mutane A Zamfara
-
Labarai2 days agoGwamnatin Tarayya Ta Ɗauki Matakan Gaggawa Bayan Tabbatar da Ebola a Birnin Tarayya
-
Labarai2 days agoGwamna Uba Sani Ya Ce Bunƙasa Ƙwarewa Na Da Muhimmanci Ga Farfaɗo Da Tattalin Arziki
-
Labarai2 days agoGwamnatin Zamfara Ta Nuna Damuwa Kan Ƙaruwar Hare-Haren ’Yan Bindiga
-
Labarai2 days agoTajudeen Zai Bayyana Rahoton Ayyukan Tinubu Cikin Kwanaki 14
-
Labarai2 days ago’Yan Sanda Sun Kama Wanda Ake Zargi da Fashi da Makami A Kano
-
Labarai2 days ago2027: Ombugadu Ya Yi Alƙawarin kawo Ƙarshen Rashin Tsaro
