Ilimi
Gwamna Namadi Ya Dauki Malaman Makaranta 2,020 Aiki
Daga Usman Muhammad
Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya miƙa takardun daukar aiki ga malaman makarantu 2,020, a wani mataki na ƙoƙarin magance ƙarancin ƙwararrun malamai a faɗin jihar.
An gudanar da bikin miƙa takardun aikin ne a Gidan Gwamnatin Jihar da ke Dutse, inda gwamnan ya bayyana cewa ɗaukar malaman zai ƙara ƙarfafa harkar koyarwa, musamman a yankunan karkara da ke fama da ƙarancin malamai.
Waɗanda suka amfana sun haɗa da tsoffin ma’aikatan shirin J-TEACH guda 1,200 da aka mayar da su ma’aikatan dindindin masu haƙƙin fansho, da kuma sababbin ma’aikatan J-TEACH guda 820 da aka ɗauka.

Namadi ya yi nuni da cewa a kwanakin baya gwamnatin jihar ta raba kayan makaranta, da suka haɗa da yunifom, jakunkuna da kayan rubutu ga dubban ɗalibai, yana mai cewa ɗaukar malaman wani mataki ne na ƙara inganta damar samun ingantaccen ilimi.
Gwamnan ya kuma sanar da raba kekuna guda 450 da wani banki ya bayar domin tallafa wa ɗaliban da ke tafiya mai nisa a ƙafa zuwa makarantu, musamman a yankunan da ke da wahalar isa. Ya ce tallafin zai taimaka wajen rage wahalar zirga-zirga, da inganta zuwa makaranta akan lokaci, halartar karatu da kuma rage yawan barin makaranta.
Ya bayyana cewa tun daga shekarar 2023, shirin J-TEACH ya samar da guraben aiki ga ma’aikata 7,500 a matakin ilimin bai ɗaya, inda aka mayar da 3,000 daga cikinsu ma’aikatan dindindin. A matakin karatun gaba da sakandare kuma, an ɗauki kusan ma’aikata 2,000, inda daga baya aka ba 1,000 daga cikinsu aikin dindindin.
Gwamna Namadi ya sake jaddada aniyar gwamnatinsa na ba da muhimmanci ga ɓangaren ilimi, ciki har da horaswa da ƙarin ƙwarewa ga malamai ta hannun Hukumar Bunƙasa Malamai ta Jihar.
Ya buƙaci Ma’aikatar Ilimi Mai Zurfi da shugabannin makarantu su tabbatar da cewa ana tura malamai bisa sahihan buƙatu, cancanta da ƙwarewar fannin da suke koyarwa, tare da kauce wa nuna bambanci tsakanin makarantun birane da na karkara.
Gwamnan ya kuma yi kira ga sababbin malaman da aka ɗauka da su kasance masu zuwa aiki akan lokaci, da ladabi da kuma jajircewa wajen sauke nauyin da ke kansu. Haka kuma, ya buƙaci sarakuna, iyaye da al’umma da su ba su goyon baya domin tabbatar da cewa kowane yaro ya samu ingantaccen ilimi.
Fassara: Safiyah Abdulkadir
-
Labarai4 days agoHukumar Alhazai Ta Jigawa Ta Bayyana Alhininta Bisa Rasuwar Suleiman Usman
-
Fasaha3 days agoNASENI Ta Ƙarfafa Horar da Sana’o’i da Fasahar Jiragen Sama Marasa Matuki a Kaduna
-
Labarai3 days agoNSCDC Ta Kama Wanda Ake Zargi Da Safarar Mutane A Zamfara
-
Labarai2 days agoGwamna Uba Sani Ya Ce Bunƙasa Ƙwarewa Na Da Muhimmanci Ga Farfaɗo Da Tattalin Arziki
-
Labarai2 days agoGwamnatin Tarayya Ta Ɗauki Matakan Gaggawa Bayan Tabbatar da Ebola a Birnin Tarayya
-
Labarai2 days agoGwamnatin Zamfara Ta Nuna Damuwa Kan Ƙaruwar Hare-Haren ’Yan Bindiga
-
Labarai2 days agoTajudeen Zai Bayyana Rahoton Ayyukan Tinubu Cikin Kwanaki 14
-
Labarai2 days ago’Yan Sanda Sun Kama Wanda Ake Zargi da Fashi da Makami A Kano
