Labarai
Gwamnatin Tarayya Ta Bada Kwangilar Aikin Sola Na ₦1bn A FUD
Daga Usman Muhammad
Gwamnatin Tarayya ta bada aikin samar da wutar lantarki mai amfani da hasken rana a Jami’ar Tarayya da ke Dutse, Jihar Jigawa, akan kudi naira biliyan ɗaya, karkashin shirin sabunta fata na Renewed Hope Solarisation Agenda.
Jami’in Hulɗa da Jama’a na jami’ar, Alhaji Abdullahi Anako, ya bayyana hakan cikin wata sanarwa, inda ya ce aikin ya ƙunshi samarwa da girka na’urar hasken rana mai ƙarfin kilowatt 500 domin inganta wutar lantarki a jami’ar.
Ya ce Hukumar Makamashi ta Najeriya ta amince da aikin, wanda ake sa ran kammala shi cikin watanni uku, kuma za a fara shi nan ba da jimawa ba.
Abdulla Anako ya ce Shugaban Jami’ar, Farfesa Ahmad Mohammed Gumel, ya bayyana godiya ga Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu da Darakta-Janar na Hukumar, Dakta Mustapha Abdullahi, bisa wannan tallafi.
Ya ƙara da cewa Hukumar a shirye take ta yi haɗin gwiwa da jami’ar wajen gudanar da bincike kan makamashin da ake iya sabuntawa.
A baya-bayan nan ne Hukumar ta amince da samar da fitilun tituna masu amfani da hasken rana guda 100 ga jami’ar, wanda a halin yanzu an samar da guda 50 daga cikinsu domin girkawa.
Fassara: Safiyah Abdulkadir
-
Labarai4 days agoHukumar Alhazai Ta Jigawa Ta Bayyana Alhininta Bisa Rasuwar Suleiman Usman
-
Fasaha3 days agoNASENI Ta Ƙarfafa Horar da Sana’o’i da Fasahar Jiragen Sama Marasa Matuki a Kaduna
-
Labarai3 days agoNSCDC Ta Kama Wanda Ake Zargi Da Safarar Mutane A Zamfara
-
Labarai2 days agoGwamna Uba Sani Ya Ce Bunƙasa Ƙwarewa Na Da Muhimmanci Ga Farfaɗo Da Tattalin Arziki
-
Labarai2 days agoGwamnatin Tarayya Ta Ɗauki Matakan Gaggawa Bayan Tabbatar da Ebola a Birnin Tarayya
-
Labarai2 days agoGwamnatin Zamfara Ta Nuna Damuwa Kan Ƙaruwar Hare-Haren ’Yan Bindiga
-
Labarai2 days agoTajudeen Zai Bayyana Rahoton Ayyukan Tinubu Cikin Kwanaki 14
-
Labarai2 days ago’Yan Sanda Sun Kama Wanda Ake Zargi da Fashi da Makami A Kano
