Labarai
Manoma 200 Sun Samu Tallafin Kayan Noma a Zamfara
Daga Ibrahim Idris Kauran Namoda
Manoma 200 daga ƙananan hukumomin Kaura Namoda da Birnin Magaji a Jihar Zamfara sun amfana da tallafin kayan noma da kuɗi daga Ɗan Majalisar Tarayya mai wakiltar mazabun biyu, Honarabul Dr. Aminu Sani Jaji.
Tallafin ya haɗa da injunan feshi, magungunan feshi, fartanya da kuma Naira dubu 50 ga kowane manomi.
Da yake jawabi a wajen rabon tallafin, Alhaji Nasiru Sani Jaji, wanda ya wakilci Hon. Dr. Aminu Sani Jaji, ya ce an samar da kayan ne domin inganta harkar noma da taimakawa wajen samar da abinci.
Ya yi kira ga manoman da suka amfana da tallafin da su yi amfani da kayan yadda ya dace domin cimma manufar da aka samar da su.
Wasu daga cikin manoman da suka amfana sun yaba wa Hon. Dr. Aminu Sani Jaji bisa kulawar da yake bai wa manoma da sauran al’umma.
Sun kuma roƙi Allah Ya saka masa da alheri tare da ci gaba da ba shi ikon tallafa wa al’umma.
Yusuf Zubairu
-
Labarai4 days agoHukumar Alhazai Ta Jigawa Ta Bayyana Alhininta Bisa Rasuwar Suleiman Usman
-
Fasaha3 days agoNASENI Ta Ƙarfafa Horar da Sana’o’i da Fasahar Jiragen Sama Marasa Matuki a Kaduna
-
Labarai3 days agoNSCDC Ta Kama Wanda Ake Zargi Da Safarar Mutane A Zamfara
-
Labarai2 days agoGwamna Uba Sani Ya Ce Bunƙasa Ƙwarewa Na Da Muhimmanci Ga Farfaɗo Da Tattalin Arziki
-
Labarai2 days agoGwamnatin Zamfara Ta Nuna Damuwa Kan Ƙaruwar Hare-Haren ’Yan Bindiga
-
Labarai2 days agoGwamnatin Tarayya Ta Ɗauki Matakan Gaggawa Bayan Tabbatar da Ebola a Birnin Tarayya
-
Labarai2 days agoTajudeen Zai Bayyana Rahoton Ayyukan Tinubu Cikin Kwanaki 14
-
Labarai2 days ago’Yan Sanda Sun Kama Wanda Ake Zargi da Fashi da Makami A Kano
