Connect with us

Kasuwanci

Uwargidan Shugaban Kasa Ta Kaddamar Da Shirin Tallafawa Mabukata.

Published

on

Shugaban shirin sabunta fata na Renewed Hope Initiative ta kasa kuma uwargidan shugaban kasar Najeriya, Sanata Oluremi Tinubu ta bada tabbacin samar da karin agaji ga marasa galihu domin rage wahalhalun da ake fuskanta a kasar.

 

Sanata Oluremi Tinubu ya bayar da wannan tabbacin ne a lokacin kaddamar da shirin raba abinci ga nakasassu da masu karamin karfi a gidan gwamnati dake Lafia babban birnin jihar Nasarawa.

 

Uwargidan shugaban kasa, wacce ta samu wakilcin uwargidan mataimakin shugaban kasa, Hajiya Nana Kashim Shettima, ta bayyana cewa baya ga mota daya, kungiyar Hope Initiative karkashin shirin tallafawa zamantakewar al’umma tana hada kai da ma’aikatar noma da raya karkara ta tarayya wajen samar da taki da sauran kayan abinci ga iyalai a cikin al’ummomi masu rauni.

 

A cewar uwargidan shugaban kasar, an kammala shirye-shiryen tabbatar da cewa mata dubu daya daga kowace daga cikin jihohi talatin da shida na tarayya sun ci gajiyar tallafin naira dubu hamsin hamsin kuma jihar Nasarawa aka dauka a matsayin wajen da za a kaddamar da shirin.

 

Sanata Oluremi Tinubu ta yabawa Gwamna Abdullahi Sule bisa goyon bayan da yake baiwa shirin Renewed Hope Initiative, inda ya kara jaddada cewa shirin da ya kunshi shirye-shiryen karfafa noma, ilimi da tattalin arziki an tsara shi ne domin bayar da tallafi ga marasa galihu a Najeriya.

 

Gwamna Abdullahi Sule wanda ya samu wakilcin mataimakinsa, Dokta Emmanuel Akabe ya yabawa uwargidan shugaban kasar bisa shirin bayar da tallafi ga marasa galihu a cikin al’umma, inda ya ce wannan matakin yana cike da alkawarin da gwamnatin tarayya ta dauka na tabbatar da cewa babu yunwa a kasar nan.

 

Yayin da yake lura da cewa tun daga lokacin gwamnatin jihar Nasarawa ta dauki matakin gwamnatin tarayya wajen raba kayan agaji ga marasa galihu domin magance wahalhalun da ‘yan kasa ke fuskanta a halin yanzu, Dokta Akabe ya bayyana fatansa na ganin an kawo karshen wannan mawuyacin hali.

 

Wadanda suka halrci wannan taron sun hada da Mai Martaba Sarkin Lafiya, Mai Shari’a Sidi Bage Mohammed mai ritaya, Shugaban Jam’iyyar APC na Jihar, Aliyu Bello da uwargidan mataimakin gwamnan jihar, Sheila Tosan Akabe da kuma ‘yar majalisa mace tilo a jihar kuma shugabar kwamitin harkokin mata na majalisar wakilai Hajarat Danyaro Ibrahim wadda ta tsaya takarar kakakin majalisar jiha da sauransu.

 

Dukkansu sun tabbatar da irin jajircewar uwargidan shugaban kasar na magance matsalolin da ‘yan kasa ke ciki.

COV/Aliyu Muraki/Lafia/Wababe

Labarai

Labarai4 days ago

Gwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, zai halarci zama na 81 na Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya...

Ilimi5 days ago

An Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo

Daga Khadijah Aliyu  Karamar Hukumar Gwarzo ta Jihar Kano ta raba kayan makaranta guda 20,243 ga ɗaliban makarantun firamare daban-daban...

Labarai6 days ago

Gwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnatin Jihar Jigawa ta sake jaddada aniyarta ta ci gaba da aiki kafada da kafada da...

Labarai6 days ago

Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya

Daga Bello Wakili, Abuja Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya dawo Najeriya bayan ya wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a...

Labarai6 days ago

UNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina

Daga Isma’il Adamu, Katsina Asusun Tallafawa Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya, UNICEF, tare da haɗin gwiwar Hukumar Ilimin Firamare ta...

Labarai6 days ago

NSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Hukumar Tsaro Farin kaya ta Najeriya, NSCDC, reshen Jihar Zamfara, ta kama wani mutum mai shekaru...

Labarai6 days ago

Majalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari

Daga KHADIJAH ALIYU, Kano Majalisar Dokokin Jihar Kano ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta tabbatar da kammala aikin...

Labarai6 days ago

Masu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki

Daga ALI MUHAMMAD RABIU Shirin Ƙarfafa Juriya Ga Sauyin Yanayi A Yankunan Busassun yankuna na Jihar Kwara, KWACReSAL, ya fara...

Ilimi7 days ago

Zamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta

Daga Aminu Dalhatu  Hukumar Ilimin Bai-daya ta Jihar Zamfara, ZSUBEB, ta kaddamar da shirin shigar da yara makaranta na shekarar...

Labarai1 week ago

Gwamnan Kebbi Ya Yabi WAMY Kan Jinya Kyauta Ga Marasa Lafiya

Daga Sani Dutsinma Gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris, ya yaba wa Ƙungiyar Matasa Musulmi ta Duniya (WAMY) kan shirya aikin...

Mafi Shahara