Ilimi
SUBEB Ta Gudanar Da Jarabawa Ga Malaman Da Ke Neman Mukaman Sakatarorin Ilimi A Jigawa
Hukumar Kula da Ilimin Firamare ta Jihar Jigawa (SUBEB) ta gudanar da zagaye na biyu na jarabawa ga malamai da ke neman mukamin sakatarorin ilimi a kananan hukumomi 27 na jihar.
Shugaban hukumar, Farfesa Haruna Musa, ne ya bayyana hakan ga manema labarai a Dutse.
A cewarsa, malamai 129 ne suka zauna jarabawar daga cikin 159 da suka rubuta zagaye na farko a Jami’ar Tarayya ta Dutse.
Farfesa Musa ya kara da cewa tambayoyin jarabawar sun shafi matsalolin da makarantun da ke karkashin hukumar ke fuskanta da kuma hanyoyin warware su.
Ya ce malamai za su kuma fuskanci jarabawar kwamfuta domin a tantance iya rubuta rahotanni da aikawa da saƙonni ta hanyar zamani.
Gidan Radio Najeriya ya ruwaito cewa an gayyaci malamai daga jami’a domin su sa ido kan jarabawar da kuma tantance waɗanda suka fi cancanta don mukamin sakataren ilimi.
Usman Mohammed Zaria
-
Ilimi6 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai5 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
-
Labarai20 hours ago
Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu
-
Labarai22 hours ago
NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta
