Labarai
Sojojin Najeriya Sun Yi Jana’izar Bangirma Ga Wani Doki A Kaduna
Runduna daya ta sojojin Najeriya ta gudanar da bikin jana’izar marigayi Mascot, Sajan Dalet Danfari Akawala, a shalkwatar rundunar dake jihar Kaduna. Wanda dokin sojojin ne.
A wata sanarwa da mukaddashin Daraktan hulda da jama’a na rundunar soji ta daya, Laftanar Kanar Musa Yahaya ya fitar, ya ce Kanar Akabike ne ya jagoranci jana’izar, wanda ya wakilci babban hafsan rundunar, Manjo Janar Mayirenso Lander David Saraso.
A cewar sa, Marigayi Sajan Dalet Danfari Akawala ya yi hidimar sashen sadaukarwa da aminci, tare da nuna jajircewa da juriya a gidan Soja.
“Bikin shi ne hanyar mu na girmamawa ta ƙarshe ga wani wanda ya kawo sauyi da farin ciki da aiki tukuru da kuma daukaka sashen da yayi aiki”
Kanar Akabike ya mika ta’aziyyarsa ga daukacin wadanda sukayi aiki da shi da sojojin Najeriya, yana mai nuna jimami game da wannan rashin da aka yi.
Ya kuma yabawa manyan baki da masu jajantawa da suka halarci bikin, yayin da aka yi addu’o’in Allah ya ba shi jajircewa, gwargwado, da kwazon maye gurbin marigayi Sajan Akawala.
A yayin bikin jana’izar, an bayyana Sajan Akawala a matsayin wanda ya fito daga zuriyar Mascot na Sashen, Sajan Farin Doki, wanda ya yi aiki daga 1995 har zuwa rasuwarsa a shekarar 2011. Bayan rasuwar Sgt Farin Doki, rundunar ta samu sabon mascot, Sgt Danfari. Akawala, wanda ya yi aiki har zuwa rasuwarsa a shekarar 2014. Sgt Danfari Akawala’s foal, Sgt Dalet.
An kammala jana’izar ne da addu’o’i da mukaddashin Daraktan (Protestant), Laftanar Kanal Ugwu ya yi, kuma ya samu halartar manyan hafsoshi, sojoji da iyalansu.
PR/Usman Sani/Wababe
-
Ilimi6 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai5 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
-
Labarai1 day ago
Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu
-
Labarai1 day ago
NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta
