Labarai
Sojin Nijar Za Su Saki Bazoum
Gwamnatin mulkin soja a Jamhuriyar Nijar ta shiga sarkakiya bayan ta amince za ta saki hambararren shugaban kasar Mohamed Bazoum da matarsa Khadija.
Babban abin da ya jefa manyan jami’an soji a Jamhuriyar Nijar cikin rudani shi ne nacewar da Bazoum ya yi na ci gaba da zama a cikin kasar ta Nijar, bisa dalilin cewa ba ya sha’awar komawa wata kasa.
Wasu mazauna birnin Yamai, babban birnin kasar, da kuma Maradi daya daga cikin manyan biranen kasar, sun ce wata fitacciyar jarida a kasar cikin harshen Faransanci ta ambato labarin shirin sojojin na sakin Bazoum.
Majiyoyin sun ce hukumomin sojin na aiki kan yadda “abubuwa za su tafi daidai”, idan har suka bar Bazoum ya ci gaba da zama a Jamhuriyar Nijar.
Wani bangare na fargabar gwamnatin mulkin sojin shi ne yiwuwar samun zanga-zanga daga masu goyon bayan hambararren shugaban kasar domin neman a ba shi cikakken ‘yanci, tun da yarjejeniyar a halin yanzu ita ce Bazoum zai gaba da kasancewa a cikin wani tsari na daurin talalar zaman gida ba fita.
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
