Ilimi
Ruwan Sama Ya Lalata Gidaje Da Makarantu A Jihar Kwara
Sama da mutane 100 ne mazauna garin Ijagbo da ke karamar hukumar Oyun ta jihar Kwara suka rasa matsugunansu sakamakon ruwan sama ya yi barna a cikin al’umma.
Gidan Rediyon Najeriya ya tattaro cewa an lalata cibiyoyin ilimi da gidajen zama da rumfunan kasuwa tare da lalata dukiyoyi.
Guguwar ruwan sama ta yi barna a kwalejin Ansar Deen da ke Ijagbo yayin da ajujuwa sama da 10 suka yi lalace, inda dalibai da malamai suka makale.
An gano cewa guguwar ta afku ne da misalin karfe 4 na yamma. a ranar Litinin, tare da yaga rufin ajujuwan tare da lalata muhimman kayan koyo da kuma kawo cikas ga ayyukan ilimi.
Da suke Magana game da wannan ibdi’in, shugabannin makarantar, Mista Olaniyi Musbaudeen da Misis Saheed, sun yi kira ga gwamna AbdulRahman AbdulRazaq da ya gaggauta kawo musu tallafi domin dawo da ababen more rayuwa da suka lalace.
“Mun yi matukar bakin ciki da wannan bala’in. Rugujewar wadannan ajujuwa na haifar da babbar barazana ga karatun dalibanmu,” in ji Mista Musbaudeen.
A halin yanzu kwamishinan ilimi na jihar Kwara Dr Lawal Olohungbebe ya ziyarci makarantar da lamarin ya shafa domin tantance irin barnar da aka yi .
Ya kuma baiwa mahukuntan makarantun da sauran al’ummar jihar tabbacin shirin gwamnatin jihar na maido da kayayyakin da abin ya shafa.
COV/ALI MUHAMMAD RABIU
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
-
Labarai6 days agoMasu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki
