Kasuwanci
Ruwa Ya Ci Rayukan Mata Biyu A Kano
Mazauna karamar hukumar Gezawa ta Kano sun shiga cikin tashin hankali da makoki sakamakon nutsewar wasu mata biyu a cikin wani tafki.
Rahotanni sun nuna cewa matan (an sakaya sunansu) sun gamu da ajalinsu ne a lokacin da suke wanka a kogi bayan sun dawo daga aiki a wata masana’antar sarrafa hibiscus.
A cewar jami’in hulda da jama’a na hukumar kashe gobara ta jihar Kano Saminu Yusif Abdullahi Gezawa hukumar kashe gobara ta samu kiran gaggawa daga ‘yan banga da ke yankin tare da bayyana cewa “Yan uwan matan biyu ne suka kai rahoton lamarin ga dan banga”
Ya yi nuni da cewa, nan take aka tura tawagar masu aikin ceto zuwa wurin, inda suka yi nasarar zakulo gawarwakin su a sume, daga bisani jami’an lafiya suka tabbatar da mutuwarsu.
Saminu ya bayyana cewa an mika gawarwakin ga wani dan sanda Musa Garba na sashin ‘yan sanda na Gezawa.
Ya shawarci jama’a da su daina zuwa kusa da kogi domin gujewa abubuwan da ba a zata ba.
KHADIJAH ALIYU
-
Ilimi6 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
-
Labarai1 day ago
Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu
-
Labarai1 day ago
NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta
