Labarai
Kwamitin Neman Sabuwar Karamar Hukumar Kanya Babba Ya Gabatar Da Takardar Bukatarsa Ga Majalisar Dattawa
Kwamitin neman sabuwar Karamar Hukumar Kanya Babba daga Karamar Hukumar Babura ta Jihar Jigawa, ya gabatar da takardar bukatarsa ga kwamitin Majalisar Dattawa mai kula da kirkiro jihohi da kananan hukumomi a zaman da aka yi a jihar Kano.

A yayin mika takardar, Shugaban kwamitin kuma Hakimin Kanya Babba, Makaman Ringim, Malam Mohammed Ibrahim ya bayyana cewar wannan yunkuri ya bi duk sharuddan da kundin tsarin mulki ya shimfida don kafa sabuwar karamar hukuma.

Makaman na Ringim ya kara da cewar, daukacin al’ummar yankin Kanya Babba, ciki da wajen mazabar na matukar goyon bayan hakan domin bunkasa ci gaban tattalin arziki da al’umma a yankin.

Da yake karbar takardar, Shugaban kwamitin Majalisar Dattawa, Sanata Barau Jibril, ya nuna jin dadin sa da jajircewar mutanen Kanya Babba wajen mika takardar.
Barau Jibrin, ya kuma tabbatar musu kwamitinsa zai yi adalci da gaskiya a aikin da aka dora musa.

Wakilinmu ya bamu rahoton cewar, taron mika bukatar ya samu halartar mataimakin Gwamnan jihar Jigawa, Injiniya Aminu Usman da Sanatan Jigawa ta Arewa maso Yamma, Alhaji Babangida Husaini da dan majalisar jiha mai wakiltar mazabar Kanya, Alhaji Ibrahim Hashim Kanya da shugaban Karamar Hukumar Babura, Alhaji Hamisu Muhammad Garu da mai bawa gwamna shawara kan harkokin bada aiyukan kwangila Usman Haladu Isa da Alhaji Salisu Muazu Kanya da hakimai da Dagatai da ‘yan siyasa da kuma sauran masu ruwa da tsaki da dimbin masoya.
Usman Mohammed Zaria
-
Ilimi6 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
-
Labarai1 day ago
Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu
-
Labarai1 day ago
NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta
