Labarai
Kwale-kwale Ya Kife Da Fasinjoji 16 A Karamar Hukumar Taura
Akalla mutane 7 ne aka ceto, bayan kifewar kwale-kwale a wani kogi da ke Zangon Maje, ƙaramar hukumar Taura, ta jihar Jigawa ranar Litinin.
Shugaban ƙaramar hukumar Taura, Dr Shuaibu Hambali ne ya bayyana hakan ga Rediyon Najeriya a Dutse, babban birnin jihar.

A cewarsa, lamarin ya faru ne da yammacin ranar Litinin, lokacin da wasu manoma ke dawowa daga gonakinsu a ƙauyen Zangon Maje, inda suka hau kwale-kwalen.
Ya ce, jami’an bada agajin gaggawa na yankin sun samu nasarar ceto mutane 7 a kokarin da suka yi na ceto wadanda lamarin ya shafa.
Ya ƙara da cewa, masu ceton sun gano gawar mutum guda a yankin Yalleman da ke ƙaramar hukumar Kaugama.

Dr Shuaibu ya bayyana cewa, sauran mutane 9 da ke cikin jirgin har yanzu ba a same su ba a lokacin da ake bayar da wannan rahoto.
Rediyon Najeriya ya ruwaito cewa, ba a fitar da sunayen waɗanda abin ya shafa ba, amma lamarin ya jefa al’ummar yankin cikin jimami da baƙin ciki.
Shugaban ƙaramar hukumar ya bayyana cewa, za a raba rigunan kariya (life jacket) ga fasinjoji a nan gaba kadan domin kiyaye sake afkuwar lamarin nan gaba.

Ya kuma gargadi matuka kwale-kwale da su kiyaye ƙa’idojin tsaro da kaucewa cunkoson fasinjoji, musamman da yamma a lokacin damina, inda ruwa ke ƙaruwa a kowane lokaci.
Dr Hambali, wanda ya isa wurin da abin ya faru, ya jajanta wa iyalan waɗanda lamarin ya rutsa da su.
Wasu daga cikin mazauna yankin da Rediyon Najeriya ta tattauna da su, sun nemi gwamnatin ta gaggauta ɗaukar matakan da suka dace, tare da inganta hanyoyin sufuri ta ruwa.
Usman Muhammad Zaria
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
-
Labarai6 days agoMasu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki
