Labarai
Jihar Jigawa Za Ta Sayo Motoci 36 Ga Mambobin Kungiyar NURTW
Gwamnatin Jihar Jigawa ta amince da fitar da kudi sama da naira miliyan 279 ga Ƙungiyar Direbobin Motocin Haya ta Najeriya (NURTW) reshen jihar Jigawa karkashin shirinta na tallafawa masu sana’o’i.
Kwamishinan Muhalli, Sabunta Makamashi da Sauyin Yanayi na jihar, Dr. Nura Ibrahim ne ya bayyana hakan yayin da yake zantawa da manema labarai bayan taron majalisar zartarwa da Gwamna Umar Namadi ya jagoranta a gidan gwamnati dake Dutse.
Ya bayyana cewa za a yi amfani da kudaden ne wajen siyan motoci Sharon guda goma sha shida da kuma motoci Golf Volkswagen guda ashirin domin raba wa mambobin ƙungiyar guda talatin da shida a matsayin tallafin dogaro da kai.
Ya ƙara da cewa, majalisar ta kuma yanke shawarar fitar da wasu karin naira miliyan 431 a matsayin tallafi ga ƙanana da matsakaitan ’yan kasuwa guda hamsin da takwas a fadin jihar.
Kwamishinan ya ƙara da cewa, akwai ƙarin aikace-aikace goma sha bakwai na kudi sama da naira miliyan goma sha tara da ake ci gaba da tantancewa.
Usman Muhammad Zaria.
-
Ilimi6 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai5 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
-
Labarai22 hours ago
Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu
-
Labarai1 day ago
NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta
