Labarai
Hukumar Alhazan Jihar Jigawa Ta Ware Kujeru 54 Ga Malamai Da Jami’an Kananan Hukumomi
Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Jigawa ta bayyana cewa Gwamna Umar Namadi ya amince da rabon kujeru 54 na Hajj ga malamai da jami’an da za su jagoranci Alhazai don aikin Hajjin 2025.
Babban Daraktan hukumar, Alhaji Ahmed Umar Labbo, ne ya bayyana hakan ga wakilin Radio Nigeria a Dutse, babban birnin jihar.

A cewarsa, Gwamna Umar Namadi ya amince da rabon kujerun ne domin bai wa jami’ai da malamai damar jagorantar Alhzan jihar a Najeriya da Saudiyya.
Alhaji Ahmed Umar Labbo ya ce, wannan tsari da hukumar ta kirkiro shi ne irinsa na farko a tarihin Jihar Jigawa.
Ya bayyana cewa, an zabi jami’an da malamai maza da mata daga daga kananan hukumomi 27 na jihar bisa cancanta.
Ya jaddada cewa, an zaɓi mutum biyu daga kowace karamar hukuma ta jihar.

Babban Daraktan ya bayyana cewa, malamai da jami’an sun samu umarni don koyar da maniyyata game da wajiban Hajj, ka’idoji da kuma manyan ginshiƙan aikin Hajj domin su san yadda za su gudanar da ibadar Hajj yadda ya kamata.
Ya bayyana cewa, bayar da cikakken horo da ilimantar da maniyyata zai taimaka musu wajen gudanar da Hajj bisa koyarwar addinin Musulunci tare da wakiltar Najeriya da kyau.
Ya ƙara da cewa, za a ci gaba da gudanar da bita ga maniyyatan Hajj na 2025 a dukkan cibiyoyin da aka kebe bayan Ramadan.
Ahmed Labbo ya ce, hukumar za ta fara raba kayayyakin tafiya ga maniyyatan Hajj na 2025 nan ba da daɗewa ba.

A cewarsa, rarraba kayayyakin tafiya wadanda suka haɗa da yunifom da jakunkuna zai fara nan gaba a hedkwatar hukumar da wasu cibiyoyi da aka ware a faɗin kananan hukumomi 27 na jihar.
Ya bayyana cewa, jirgin farko na jigilar maniyyatan jihar zai tashi a watan Mayu 2025 kamar yadda Hukumar Hajj ta Kasa (NAHCON) ta tsara.
Labbo ya jaddada cewa, NAHCON ta ba Max Air damar jigilar maniyyatan jihar zuwa Saudiyya ta filin jirgin sama na Nuhu Muhammadu Sunusi International Airport.
Shugaban Hukumar Jin Daɗin Alhazan ya gode wa Gwamna Umar Namadi bisa goyon baya da haɗin kai da yake bai wa hukumar a kowane lokaci.
USMAN MUHAMMAD ZARIA
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai7 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai7 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Labarai7 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
-
Labarai7 days agoMasu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki
-
Labarai5 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
