Labarai
Hukumar Alhazai Ta Kaduna Ta Nemi Goyon Bayan Sarkin Zazzau Don Nasarar Aikin Hajjin Bana
Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Kaduna (KSPWA) ta yaba da gudunmuwar da Gwamnatin Jihar Kaduna Malam Uba Sani ya ke badawa wajen samun nasarorin da aka samu kwanan nan.
An bayyana hakan ne a yayin wata ziyarar girmamawa da Shugaban Hukumar Jindadi Alhazai na Jihar Kaduna, Malam Salihu S. Abubakar ya jagoranta tare da tawagar Kwamitin Musamman na Hajji da shugabannin ga Sarkin Zazzau, Malam Nuhu Bamalli, a fadarsa da ke Zariya.
Babban burin ziyarar shi ne neman ci gaba da samun goyon baya da addu’o’in Sarkin don samun nasarar ayyukan Hajji na shekarar 2025.
Malam Salihu ya nuna godiya sosai ga gudunmuwar da Sarkin ya ba da a baya kan shirye-shiryen Hajji, tare da jaddada muhimmancin cigaba da wannan hadin kai.
Ya ce, “Goyon bayan Gwamnatin Jihar Kaduna ga jin dadin alhazanmu abin alfahari ne. Tallafi daga dukkan fannoni, ciki har da na kudi ya taimaka mana sosai wajen cimma nasarorinmu. Wannan irin goyon bayan ya bambanta Hukumar ta Kaduna da takwarorinta.”
Malam Salihu ya kara da cewa hukumar ta riga ta yi rijistar alhazai 3,480 don lokacin Hajji mai zuwa kuma ta kaddamar da shirin wayar da kan alhazai.
Wannan shirin yana da nufin ilmantar da alhazai game da yadda ake gudanar da ibadar Hajji, dokoki, da koyarwar addinin Musulunci.
A nasa jawabin, Sarkin Zazzau, Malam Ahmad Nuhu Bamalli, ya yabawa Kwamitin Musamman na Hajji kan gyare-gyaren da suka kawo a hukumar.
Ya jaddada cewa wadannan gyare-gyaren suna da matukar muhimmanci wajen tabbatar da cewa alhazan sun amfana da kudaden da suka kashe wajen tafiya Saudiyya.
Sarkin ya yi kira da a ilmantar da alhazai kan haramcin daukar kaya haram zuwa Kasar Saudiyya don kauce wa samun matsala da hukumomin Saudiyya.
Ya kuma roki Ofishin Jakadancin Najeriya da ke Saudiyya da su ci gaba da yin aiki tare da Hukumar Hajji ta Kasa domin tabbatar da cewa alhazan Najeriya sun samu kima da mutunci a tsawon zamansu.
Rel/Adamu Yusuf
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
-
Labarai6 days agoMasu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki
