Labarai
Gwamnatin Tarayya Ta Bukaci Al’umma Da Su Rika Taimakawa Hukumomin Tsaro Da Muhimman Bayanai
Gwamnatin Tarayya ta yi kira ga ‘yan Najeriya da su rika ba da muhimman bayanai ga hukumomin tsaron kasar nan.
Ministan tsaro, Alhaji Badaru Abubakar ne ya yi wannan kiran a lokacin da yake jawabi a wani taron jama’a na gwamnatin jihar Jigawa da aka gudanar a karamar hukumar Birnin Kudu.

A cewar sa, kiran ya zama wajibi domin karfafa tsaro a fadin Najeriya.
Alhaji Badaru Abubakar, ya yi nuni da cewa an samu ingantuwar harkokin tsaro a fadin kasar cikin ‘yan watannin nan.

Ya kuma bayyana cewa, gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu ta yi iya bakin kokarinta wajen yaki da rashin tsaro, kuma za ta ci gaba da jajircewa wajen cimma manufofin da ake so.
Ministan ya yi nuni da cewa, gwamnatin tarayya za ta ci gaba da bayar da duk wani tallafi ga sojojin Najeriya da ke fagen fama don tabbatar da an maido da tsaro.


Badaru Abubakar wanda shi ne tsohon gwamnan jihar Jigawa, ya bayyana jin dadinsa da yadda ya mika ragamar shugabanci ga gwamnati mai inganci.
Ya yabawa gwamnatin Gwamna Umar Namadi bisa gagarumin ayyukan raya kasa da aka gudanar a jihar cikin shekara daya da rabi.

“Na yi farin cikin ganin manyan ayyukan raya kasa da wannan gwamnati ta aiwatar, a cikin shekara daya da rabi da ta wuce,” in ji Ministan.
Gidan rediyon Najeriya ya ruwaito cewa, wasu daga cikin manyan baki da suka halarci bikin sun hada da, mataimakin gwamnan jihar, Injiniya Aminu Usman, da tsohon gwamnan jihar Barista Ali Sa’ad Birnin Kudu, da sakataren gwamnatin jihar Malam Bala Ibrahim, da sarakuna da malaman addinai, da manyan jami’an gwamnati da dai sauransu.
Usman Muhammad Zaria.
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
-
Labarai6 days agoMasu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki
