Kasuwanci
Gwamnatin Kano Zata Kashe Naira Miliyan Dubu 51 Don Aiwatar Da Ayukka
Majalisar zartaswar jihar Kano ta amince da kashe Naira biliyan 51.5 wanda ba a taba ganin irinsa ba, domin muhimman ababen more rayuwa da ayyukan yi wa al’umma hidima a fadin jihar, a wani bangare na tsare-tsare na gwamnatin na bunkasa zamantakewa da tattalin arziki.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa ya fitar bayan taron majalisar zartarwa karo na 27 da aka gudanar a gidan gwamnatin Kano.
A cewar sanarwar, majalisar ta ba da haske ga manyan ayyuka da yawa, da suka hada da manyan gyare-gyaren hanyoyi, shigar da tsarin zirga-zirga, fadada gine-ginen jama’a, da inganta wutar lantarki.
Wani abin lura a cikin amincewar akwai fitar da naira biliyan 5.4 domin gyaran tituna da kwalta da suka tashi daga gidan Mumbayya zuwa Mahadar Tal’udu, Gadon Kaya, titin Yahaya Gusau, da Titin Sharada.
An kuma ware Naira biliyan 3.4 don samar da fitilun masu amfani da hasken rana a fadin birnin Kano a karkashin shirin sabunta birane.
An amince da karin wasu kudade don gina titin Miller zuwa titin Mishan da kuma gyara wasu muhimman kayayyakin aikin gwamnati da suka hada da Sashen Albarkatun Ilimi na Kano da Gidan Gwamna da ke Kaduna.
Majalisar ta kuma amince da Naira Biliyan 1.46 don ingantawa da kuma zamanantar da ma’aikatar Wutar Lantarki da Sabunta Makamashi da ke cikin Sharada.
Sanarwar ta ce “Wadannan amincewar sun nuna kudurin gwamnatin na samar da ci gaba mai dorewa a birane da kuma inganta ayyukan jama’a.”
Abdullahi Jalaluddeen/Kano
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
-
Labarai6 days agoMasu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki
