Fasaha
Gwamnan Kano Ya Kaddamar da Shirin Dashen Bishiyoyi
Gwamnatin jihar Kano ta jaddada kudirinta na yaki da gurbacewar kasa, zaizayar kasa da sauran kalubalen muhalli.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayyana hakan ne a yayin bikin kaddamar da wani katafaren shirin dashen itatuwa, inda za a dasa itatuwa miliyan 5 da rabi a fadin jihar, wanda aka gudanar a karamar hukumar Makoda.
Ya ce babban makasudin wannan shirin shi ne a magance dimbin kalubalen muhalli da ke addabar al’ummar jihar Kano.
Gwamna Yusuf ya jadadda cewa wadannan kalubalen na haifar da babbar matsala ga al’umma.
Gwamnan ya tabbatar da cewa gwamnatin jihar ta bayar da duk wani tallafin da ya dace don shayar da ‘ya’yan itatuwan, ta yadda za su yi girma da kuma cim ma burin da aka yi niyya. Wannan tallafi yana da mahimmanci don nasarar shirin.
Ya bukaci dukkan shugabannin kananan hukumomi 44, shugabannin gargajiya, da jami’an ci gaban al’umma (CDOs) da su sanya hannu a cikin wannan shirin, inda ya ce shigar su na da matukar muhimmanci wajen cimma manufofin shirin.
“Idan aka kula da kyau itatuwan da aka dasa ta wannan shiri za su taka rawar gani wajen magance sauyin yanayi da batutuwan da ke da alaka da hakan. Hakan ya yi dai-dai da manyan manufofin jihar Kano.”
Kwamishinan Muhalli, Dr. Dahiru Mohammad Hashim, ya yaba da kudurin Gwamna Yusuf na tallafawa kokarin ma’aikatar wajen dakile matsalolin muhalli.
Sarkin Dawakin Mai Tuta Alhaji Mohammad Bello Abubakar, wanda ya wakilci Mai Martaba Sarkin Kano, Alhaji Muhammad Sanusi II ya jaddada goyon bayan Masarautar kan shirin dashen itatuwa.
Taron ya gabatar da bayar da kyautuka ga mutanen da suka bayar da gudunmawa sosai wajen tallafawa al’ummarsu.
Wannan amincewa yana aiki azaman abin ƙarfafawa ga wasu don shiga cikin ayyukan muhalli.
ABDULLAHI JALALUDDEEN KANO
-
Ilimi5 days agoGwamna Namadi Ya Dauki Malaman Makaranta 2,020 Aiki
-
Labarai2 days agoƊan Takarar Gwamnan Accord A Kebbi Ya Yi Alƙawarin Ƙara Albashin Ma’aikata Zuwa N500,000
-
Labarai2 days agoGwamna Dauda Lawal Ya Ƙaddamar Da Gina Hanyar Kilomita 95 A Tsafe Don Ƙarfafa Ayyukan Tsaro
-
Labarai2 days agoGwamna Kefas Ya Zargi Jami’an Gwamnatinsa Da Taimaka Wa Haƙar Ba Bisa Ka’ida Ba
-
Labarai21 hours agoGwamnatin Jigawa Za Ta Kafa Cibiyar Ayyukan Noma Da Samar Sa Kayayyakin Zamani
-
Labarai2 days agoUNILORIN Ta Zama Ta Farko A Najeriya Wajen Ingancin Bincike
-
Labarai22 hours agoGwamnatin Jigawa Za Ta Biya Diyar Naira Miliyan 982 Ga Wadanda Aikin Hanya Ya Shafa
-
Labarai22 hours agoGwamnatin Jigawa Ta Amince Da Gudanar Da Ayyukan Kiwon Lafiya Na Miliyoyin Naira
