Ilimi
Gwamnan Kano Ya Bada Umarnin Bincika Zargin Zaftare Albashin Ma’aikatan Gwamnati.
Gwamna Abba Yusuf na jihar Kano ya yi wani kakkausan gargadi game da rahotannin rashin biyan albashi da rashin biyan ma’aikatan jihar, inda ya bayyana hakan a matsayin tauye hakkin ma’aikata da kuma cin amanar jama’a.
Gwamnan ya bayyana haka ne a lokacin da yake kaddamar da kwamitin bincike mai mutane bakwai, karkashin jagorancin Hon. Abdulkadir Abdussalam, domin gano musabbabin sabanin.
Sakataren gwamnatin jiha Alhaji Umar Faruk ya wakilta, ya ce kwamitin ya hada da manyan jami’an gwamnati da masana harkokin kudi da wadanda suka kware a tsarin biyan albashi.
Yace Membobin Kwamitin sune Abdulkadir Abdussalam_ – Shugaban, Kwamishinan Karkara da Ci gaban Al’umma Dr. Bashir Abdu Muzakkari – memba, mai ba da shawara na musamman kan tattalin arzikin dijital, Dr. Aliyu Isa Aliyu – Memba, Darakta-Janar na Ofishin Kididdiga na Jihar Kano.
Dokta Hamisu Sadi Ali, Memba, Babban Darakta Janar na Ofishin Kula da Bashi na Jihar Kano, Hajiya Zainab Abdulkadir – Mamba, Darakta, Cibiyar Kwamfuta ta Jihar Kano, Aliyu Muhammad Sani – Sakatare, Darakta, Bincike da Aiki na Hukumar REPA, Ofishin SSG.
Ummulkulthum Ladan Kailani – zata kasance mataiamakiyar sakataren kwamitin.
Ya ce an baiwa kwamitin kwanaki bakwai don gabatar da cikakken rahoto.
Gwamnan ya kuma tabbatar wa da ma’aikatan gwamnati cewa gwamnatinsa ta himmatu wajen tabbatar da adalci, gaskiya da kuma biyan albashi cikin gaggawa, yana mai gargadin cewa duk wanda aka samu da laifin cin zarafin ma’aikata zai fuskanci mummunan sakamako.
ABDULLAHI JALALUDDEEN KANO
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
