Connect with us

Fasaha

Ana Neman Daukar Karin Matakin Kawar Da Shingayen Dake Hana ‘Ya’ya Mata Zuwa Makaranta A Zamfara

Published

on

Mahalarta taron masu ruwa da tsaki na yini daya don tabbatar da sakamakon bincike kan al’amuran zamantakewa da suka shafi ilimin ‘ya’ya mata a jihar Zamfara, sun bukaci iyaye, shugabannin al’umma, da gwamnati a dukkan matakai da su magance matsalolin da ke hana yara mata zuwa kammala karatun sakandare.

 

Kungiyar AGILE da ke Jihar Zamfara tare da hadin gwiwar Media and Publicity Consult ta shirya taron masu ruwa da tsaki na rana daya domin tabbatar da sakamakon binciken da aka yi kan ka’idojin zamantakewa da ke kawo cikas ga ’yan mata matasa da ke hana shiga makarantun gaba da sakandare a jihar Zamfara.

 

Da yake jawabi a wajen taron, Farfesa Abubakar Aliyu Liman na Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya, ya jaddada bukatar masu ruwa da tsaki su samar da yanayi mai kyau da zai karfafa gwiwar ‘ya’ya mata su ci gaba da karatu.

 

Farfesa Liman, wanda kuma shi ne babban mai ba da shawara kan aikin bincike na AGILE a Zamfara, ya bayyana cewa auren dole da rashin goyon bayan iyaye a matsayin wasu manyan matsalolin da suka shafi ilimin ‘ya’ya mata a jihar.

 

 

Wakilan Ma’aikatun Mata da Ilimi na Jihar Zamfara sun yaba da tasirin aikin AGILE a Zamfara tare da yin kira da a ci gaba da inganta ayyukan da suka hada da samar da ingantattun hanyoyin ruwa, tsaftar muhalli a makarantu.

 

Mataimakin kodinetan hukumar AGILE a jihar Zamfara, Dakta Salisu Dalhatu, ya bayyana cewa an kammala makarantu 317 daga cikin 440 da aka ware domin gyarawa a karkashin hukumar ta AGILE, yayin da sama da ‘yan mata 8,000 ke cin gajiyar shirin bayar da tallafin kudi.

 

Manajan Daraktan yada labarai da tuntuba (MPC), Malam Nasiru Usman Biyabiki, ya ce taron tabbatar da shi an yi shi ne da nufin tace sakamakon binciken don samun ingantacciyar hanyar shiga tsakani.

 

A cewarsa, gangamin wayar da kan jama’a ya taimaka wajen ganin jihar Zamfara ta kasance cikin jerin jahohi biyar da suka fi aiwatar da ayyukan AGILE a fadin kasar nan.

 

Taron wanda MPC ta kira, ya kuma yi nazari kan sakamakon da Daraktar ICT ta kungiyar, Hibban Buhari ta gabatar, wanda ya bayyana talauci, al’adu, auren dole, da rashin ingantaccen tsarin karatu a matsayin manyan abubuwan da ke kawo tarnaki ga ‘ya’ya mata da kuma rike su.

 

Binciken ya ba da shawarar yin amfani da harsunan Hausa, Fulfulde, da Larabci wajen kamfen na wayar da kan jama’a, inda rediyon ya zama cibiyar farko saboda yawan isar da sako.

AMINU DALHATU.Gusau

Labarai

Labarai4 hours ago

Gwamnatin Jigawa Za Ta Kafa Cibiyar Ayyukan Noma Da Samar Sa Kayayyakin Zamani

Daga Usman Muhammad Zaria  Majalisar Zartarwar Jihar Jigawa ta amince da sakin Naira Biliyan 7.4 domin biyan ragowar kuɗaɗen kayan...

Labarai4 hours ago

Gwamnatin Jigawa Ta Amince Da Gudanar Da Ayyukan Kiwon Lafiya Na Miliyoyin Naira

Daga Usman Muhammad Zaria Gwamnatin Jihar Jigawa ta amince da bayar da kwangilolin ayyukan kiwon lafiya da samar da abinci...

Labarai4 hours ago

Gwamnatin Jigawa Za Ta Biya Diyar Naira Miliyan 982 Ga Wadanda Aikin Hanya Ya Shafa

Daga Usman Muhammad  Gwamnatin Jihar Jigawa ta amince da biyan sama da naira miliyan 982 a matsayin diyya ga masu...

Labarai2 days ago

Gwamna Dauda Lawal Ya Ƙaddamar Da Gina Hanyar Kilomita 95 A Tsafe Don Ƙarfafa Ayyukan Tsaro

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya ƙaddamar da aikin gina sabuwar hanya mai tsawon kilomita 95...

Labarai2 days ago

Gwamna Kefas Ya Zargi Jami’an Gwamnatinsa Da Taimaka Wa Haƙar Ba Bisa Ka’ida Ba

Daga Sani Sulaiman, Jalingo Gwamnan Jihar Taraba, Agbu Kefas, ya zargi wasu jami’an gwamnati da hannu wajen taimaka wa ayyukan...

Labarai2 days ago

Ɗan Takarar Gwamnan Accord A Kebbi Ya Yi Alƙawarin Ƙara Albashin Ma’aikata Zuwa N500,000

Daga Sani Haruna Dutsin-ma, B/Kebbi Ɗan takarar jam’iyyar Accord na kujerar gwamnan Jihar Kebbi, Alhaji Muhammad Sani Abdullahi Bunza, ya...

Labarai2 days ago

UNILORIN Ta Zama Ta Farko A Najeriya Wajen Ingancin Bincike

Daga Ali Muhammad Rabi’u, Ilorin Jami’ar Ilorin (UNILORIN) ta zama jami’ar da ta zo ta farko a Najeriya wajen ingancin...

Ilimi4 days ago

Gwamna Namadi Ya Dauki Malaman Makaranta 2,020 Aiki

Daga Usman Muhammad  Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya miƙa takardun daukar aiki ga malaman makarantu 2,020, a wani...

Labarai6 days ago

Gwamnatin Tarayya Ta Bada Kwangilar Aikin Sola Na ₦1bn A FUD

Daga Usman Muhammad Gwamnatin Tarayya ta bada aikin samar da wutar lantarki mai amfani da hasken rana a Jami’ar Tarayya...

Labarai7 days ago

Mutun Uku Sun Rasu A Wani Turmutsitsi A Gidan Gwamnatin Neja

Daga Aliyu Lawal, Minna Mutane uku sun rasa rayukansu sakamakon turmutsitsi da ya auku a harabar Gidan Gwamnatin Jihar Neja...

Mafi Shahara