Ilimi
Gidauniyar Malam Bukar Ta Gudanar Da Taron Bita Ga Malaman Tafsiri Da Ke Babura
Gidauniyar Malam Bukar mai kula da hidimar al’amuran da suka shafi karantar da Alqur’ani da dake Babura ta gudanar da bitar yini 4 ga Malamai masu Tafsiri da Alarammomi a garin Babura dake Jihar Jigawa.

Da yake jawabi yayin rufe bitar, Shugaban gidauniyar, Sheikh Gwani Dr Murtala Bashari yace an shirya bitar ne da nufin kara zaburar da juna da kuma nusar da masu gabatar da tafsirin Alkur’ani kan maida hankali wajen karfafa bin abin Alkur’ani da Sunnar Manzon Allah don kaucewa fadawa miyagun akidu.

Shugaban Wanda jami’in gudanar da Shirin, Dr Ismail Ali kura ya wakilta, ya yabawa mahalarta bitar da jagororinsu bisa kwazonsu.

Shi ma a nasa jawabin, bako na musamman Farfesa Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemu ya ce bitar ta zo a dai dai lokacin da ake fuskantar kalubale na rashin kyakkyawar fahimtar wasu ma’anoni na Alkur’ani da Sunnah.
A don haka, ya bukaci malaman da su kasance a cikin neman ilimi da nazari a koda yaushe.
Hakimin Babura Sarkin Ban Ringim, Alhaji Muhammad Nata’ala Mustapha ya bukaci Malamai da su kara zaburar da iyaye kan muhimmamcin ilimin addinin musulunci ga ‘ya’yansu.
Sai dai kuma, ya koka kan yadda ‘ya’ya mata suka fi maza zuwa islamiyya, knda ya bukaci iyaye su kula domin samun ingantaccen rayuwa.
Daga cikin darussan da malaman suka gabatar yayin bitar sun hada da ilimin da ya kamata mai tafsiri ya samu, da kuma kura-kuran da mai tafsiri ke samu a lokacin karatu.
Usman Mohammed Zaria
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
