Connect with us

Labarai

An Bukaci Asusun JICHIMA Ya Fadada Hanyoyin Samun Kudade Baya Ga Gwamnatin Jigawa

Published

on

Kwamatin harkokin lafiya na majalisar dokokin jihar Jigawa ya ce gyaran fuskar da aka yiwa dokar da ta kafa asusun adashen gata na kiwon lafiya na jihar ya sahalewa asusun damar samo kudade daga wasu bangarori da ba na gwamnati ba.

Shugaban kwamatin kuma wakilin mazabar Guri, Alhaji Usman Abdullahi Tura Musari, ya yi wannan tsokaci lokacin da ya jagoranci ‘yan kwamatin domin ziyarar aiki a ofishin asusun da ke Dutse.

Ya bayyana bukatar ganin asusun JICHIMA ya nemo kudade daga hannun masu taimakon al’umma da cibiyoyi da ‘yan siyasa da kwamitocin zakka da na waqafi domin bunkasa asusun, ta yadda zai biya bukatun kiwon lafiyar al’ummar jihar.

Alhaji Usman Musari ya lura cewar fadada hanyoyin samun kudade ga asusun JICHIMA fiye da abinda ake yanka daga albashin ma’aikata zai tabbatar da ingancin aiki da kuma dorewar asusun.

Daga nan sai Alhaji Usman Musari ya shawarci asusun JICHIMA da ya rubanya kokari wajen kafa ofishinsa a dukkan kananan hukumomin jihar 27 domin biyan bukatun wadanda su ka yi rijista da asusun.

A nasa jawabin, wakilin mazabar Gwiwa Alhaji Aminu Zakari ya yi kira ga asusun JICHMA da ya inganta ayyukan sa a dukkan asibitocin da aka yiwa rijista domin gudanar da ayyukan asusun kamar yadda doka ta tanadar.

Da ya ke mayar da jawabi, Shugaban  Asusun Inshorarar Lafia na jihar Jigawan, Pharmacist Hamza Maigari Kakudi ya ce an kafa asusun ne da nufin kawar da nakasu wajen kiwon lafiyar jama’a ta hanyar tabbatar da cewar masu rauni a cikin al’umma sun samu kulawar da ta kamata.

Ya ce asusun yana shirin kaddamar da gangamin wayar da kan jama’a domin yin rijista ga masu karamin karfi 1000 a kowacce mazaba, domin cimma kudurin gwamnatin Malam Umar Namadi na kula da lafiyar jama’a.

A lokacin ziyaran, jami’an JICHIMA da kwamatin majalisar sun tattaunawa kan batun samar da ofis na dindindin ga asusun.

Usman Mohammed Zaria

Labarai

Labarai20 hours ago

Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu

Daga Nasir Malali  Dakarun Sashe na biyu na Rundunar Haɗin Gwiwa ta Arewa maso Yamma, Operation FANSAN YAMMA, sun ceto...

Labarai22 hours ago

NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta

Daga Yusuf Zubairu, Kaduna Hukumar Raya Yankin Arewa Maso Yamma ta bayyana dawo da tsaro a matsayin babban fifikonta a...

Labarai5 days ago

Gwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, zai halarci zama na 81 na Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya...

Ilimi6 days ago

An Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo

Daga Khadijah Aliyu  Karamar Hukumar Gwarzo ta Jihar Kano ta raba kayan makaranta guda 20,243 ga ɗaliban makarantun firamare daban-daban...

Labarai1 week ago

Gwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnatin Jihar Jigawa ta sake jaddada aniyarta ta ci gaba da aiki kafada da kafada da...

Labarai1 week ago

Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya

Daga Bello Wakili, Abuja Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya dawo Najeriya bayan ya wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a...

Labarai1 week ago

UNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina

Daga Isma’il Adamu, Katsina Asusun Tallafawa Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya, UNICEF, tare da haɗin gwiwar Hukumar Ilimin Firamare ta...

Labarai1 week ago

NSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Hukumar Tsaro Farin kaya ta Najeriya, NSCDC, reshen Jihar Zamfara, ta kama wani mutum mai shekaru...

Labarai1 week ago

Majalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari

Daga KHADIJAH ALIYU, Kano Majalisar Dokokin Jihar Kano ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta tabbatar da kammala aikin...

Labarai1 week ago

Masu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki

Daga ALI MUHAMMAD RABIU Shirin Ƙarfafa Juriya Ga Sauyin Yanayi A Yankunan Busassun yankuna na Jihar Kwara, KWACReSAL, ya fara...

Mafi Shahara