Labarai
An Ba Shugaba Tinubu Shawarar Kafa Sansanin Soja a Jihar Neja — Shugaban CAN
An shawarci Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu da ya kafa cikakken sansanin soja a Ƙaramar Hukumar Agwara ta Jihar Neja, wanda zai haɗa da rundunar sojoji masu kai daukin gaggawa da motocin yaƙi masu sulke, domin samun damar bibiyar ’yan bindiga tare da kawar da su duk lokacin da suka fito daga maboyarsu a cikin gandun dajin ajiyar namun daji.
Shugaban Ƙungiyar Kiristoci ta Nijeriya (CAN), reshen Jihar Neja, kuma Bishop na Cocin Katolika na Diocese na Kontagora, Reverend Bulus Dauwa Yohanna, ne ya bayar da wannan shawara yayin da yake zantawa da ’yan jarida a Ƙaramar Hukumar Suleja kan hare-haren da ke ci gaba da faruwa a ƙananan hukumomin Agwara da Borgu. Ya jaddada cewa lokaci ya yi da za a ɗauki mataki cikin gaggawa.
Reverend Bulus Yohanna ya kuma buƙaci Gwamnatin Tarayya da ta tura isassun jami’an tsaro, ta samar da dukkan kayan aikin da ake buƙata, tare da haɗa kai da masu ruwa da tsaki na yankin domin dawo da zaman lafiya. Haka nan ya nemi a ƙarfafa ofisoshin ’yan sanda da wuraren bincike ba tare da ɓata lokaci ba.
Malamin ya kuma ba da shawarar a tura ƙarin ’yan sanda zuwa ofishin ’yan sanda na Ƙaramar Hukumar Agwara, tare da samar musu da motocin aiki domin samun sakamako mafi kyau.
A nasa jawabin, ɗan marigayi Sarkin Borgu, Yarima Murtala Haliru Dantoro, ya roƙi Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya kawo musu ɗauki cikin gaggawa, domin gujewa lalacewar tarihinsu, al’adunsu, ɗabi’unsu da hanyoyin rayuwarsu sakamakon hare-haren ’yan bindiga. Ya ce ’yan bindigar na kashe mutane ba tare da la’akari da addininsu—Musulunci ko Kiristanci—ba.
Yarima Murtala Haliru Dantoro ya bayyana alhininsa kan yadda sama da mutane ɗari uku daga ƙananan hukumomin Borgu da Agwara suka rasa rayukansu, yayin da aka sace da dama, tare da lalata dukiyoyi da darajarsu ta kai miliyoyin naira. Ya yi amfani da damar wajen tunatar da Shugaban Ƙasa cewa lakabin Jagaban Borgu da aka ba shi yana ɗauke da babbar daraja da alaka mai tsarki tsakaninsa da al’ummar Masarautar Borgu, don haka ya dace ya ƙara ƙaimi wajen ceto al’ummar wannan masarauta daga hare-haren ’yan ta’adda.
Wakilin al’ummar Musulmi daga yankin, Mohammed Ibrahim Sani, ya nuna damuwarsa kan halin da ake ciki, yana mai cewa matsalar rashin tsaro ta durƙusar da ilimi, noma da hanyoyin samun abin rayuwa. Ya ƙara da cewa ’yan ta’adda na yin zirga-zirga ba tare da wata ƙalubale ba.
COV: Aliyu Lawal
-
Labarai4 days agoHukumar Alhazai Ta Jigawa Ta Bayyana Alhininta Bisa Rasuwar Suleiman Usman
-
Fasaha3 days agoNASENI Ta Ƙarfafa Horar da Sana’o’i da Fasahar Jiragen Sama Marasa Matuki a Kaduna
-
Labarai3 days agoNSCDC Ta Kama Wanda Ake Zargi Da Safarar Mutane A Zamfara
-
Labarai2 days agoGwamnatin Tarayya Ta Ɗauki Matakan Gaggawa Bayan Tabbatar da Ebola a Birnin Tarayya
-
Labarai2 days agoGwamna Uba Sani Ya Ce Bunƙasa Ƙwarewa Na Da Muhimmanci Ga Farfaɗo Da Tattalin Arziki
-
Labarai2 days agoGwamnatin Zamfara Ta Nuna Damuwa Kan Ƙaruwar Hare-Haren ’Yan Bindiga
-
Labarai2 days agoTajudeen Zai Bayyana Rahoton Ayyukan Tinubu Cikin Kwanaki 14
-
Labarai2 days ago2027: Ombugadu Ya Yi Alƙawarin kawo Ƙarshen Rashin Tsaro
