Ilimi
Kwamandan NDA Ya Bukaci Dalibai Su Dage da Karatu a Taron FGC Malali
Kwamandan, Kwalejin Horas da kananan Hafsoshin Soja ta kasar da ke Kaduna, Manjo Janar Abdul Khalifa Ibrahim ya bukaci dalibai da su jajirce wajen ganin sun samu nagartar ilimi.
Manjo Janar Abdul Khalifa Ibrahim ya yi wannan kiran ne a yayin bikin yaye dalibai da jawabai da kuma bayar da kyaututtuka da aka yi a Kwalejin Gwamnatin Tarayya ta Malali Kaduna.
Kwamandan NDA wanda tsohon dalibi ne a kwalejin ya bayyana jin dadinsa da yadda dalibai ke gudanar da ayyukansu ya yabawa mahukunta da ma’aikatan FGC Kaduna bisa yadda suke kiyaye ka’idoji.
A nasa jawabin shugaban kungiyar tsofaffin dalibai ta FGC Kaduna, Kwamared Seyi Gambo ya ce kungiyar za ta ci gaba da bayar da gudummawar ta wajen daukaka darajar kwalejin ta hanyar daukar matakai na koyar da dalibai.
Shima da yake jawabi, shugaban taron kuma tsohon gwamnan jihar jigawa, Sanata Saminu Turaki ya bukaci dalibai da su tabbatar sun yi fice a fannin ilimi domin su zama masu amfani a cikin al’umma.
Shima da yake jawabi shugaban kwalejin gwamnatin tarayya ta Kaduna, Prince Adewale O. Adeyanju ya yi kira ga iyaye da su bada hadin kai ga hukumar makaranta domin ganin an kula da harkokin koyo.
An bayar da kyautuka na kyaututtuka da kudi ga daliban da suka kammala karatunsu da nagartattun dalibai da suka hada da malamai da suka kware sosai da kuma ma’aikatan da ba na koyarwa a kwalejin.
COV/SHETTIMA A.
-
Ilimi6 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
-
Labarai1 day ago
Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu
-
Labarai1 day ago
NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta


