Ilimi
Gwamnatin Kano Ta Kaddamar Da Bincike Kan Mutuwar Dalibai Biyu A Makaranta
Gwamnatin Jihar Kano ta kaddamar da bincike kan mutuwar ban mamaki ta wasu dalibai biyu a Kwalejin Sakandaren Gwamnati ta kwana da ke Bichi, wato Hamza Idris Tofawa da Umar Yusuf Dungurawa.
Rahotanni sun ce wasu daliban makarantar ne suka kai musu hari da wani irin l ƙarfe da ake kira “Gwale-Gwale”.
Lamarin ya tayar da ƙura inda al’umma a fadin jihar suka nemi a tabbatar da adalci game da lamarin.
Yayin da yake magana da manema labarai a madadin Kwamishinan Ilimi Dr. Ali Haruna Makoda, Babban Sakataren Ma’aikatar Ilimi, Alhaji Bashir Baffa Muhammad, ya bayyana cewa gwamnati ta ɗauki lamarin da muhimmanci kuma ba za ta yi sakaci ba wajen tabbatar da adalci.
“Gwamnatin Jihar Kano za ta gudanar da bincike busa gaskiya, da adalci. Mun sha alwashin ganin an tabbatar da adalci ga dukkan wadanda lamarin ya shafa.” Inji shi
Ya ja hankalin dalibai da su guji ɗaukar doka a hannunsu, su riƙa kai koke-kokensu ga mahukuntan makaranta.
Babban Sakataren ya kuma miƙa ta’aziyyar gwamnati ga iyalan mamatan, tare da addu’ar samun rahama garesu.
Shugaban Sashen Makarantun Sakandare na Hukumar Gudanar da Makarantun Sakandare ta Jihar Kano, Malam Abbas Abdullahi, ya bayyana matakin da aka ɗauka a matsayin abin takaici inda ya gargadi dalibai su guji yin amfani da matsayinsu wajen cutar da wasu da kuma aikata tashin hankali.
Wani ɗan uwa ga ɗaya daga cikin mamatan, Malam Ibrahim Yusuf Dungurawa, ya bayyana irin radadin da suka shiga bayan samun labarin mutuwar ɗansu, tare da roƙon gwamnati da ta tabbatar da adalci.
Haka zalika, mahaifin ɗaya daga cikin daliban da suka rasu, Malam Idris Garba Tofawa, ya ce sun ɗauki lamarin a matsayin ƙaddarar Ubangiji, amma ya bukaci hukumomi da su ɗauki matakin gaggawa don hana maimaituwar irin wannan lamari.
Ya ce: “Muna roƙon a tabbatar da adalci, ba don ɗanmu kaɗai ba, har ma da lafiyar sauran dalibai gaba ɗaya.”
Yayin da ake ci gaba da bincike, Gwamnatin Kano ta sake jaddada kudirinta na kare lafiyar dalibai da kuma tabbatar da doka da oda a dukkan makarantun gwamnati.
Ana sa ran hukumomin tsaro za su ba da goyon baya wajen gudanar da binciken da kuma tabbatar da cewa an hukunta masu laifi.
Khadijah Aliyu
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai7 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai7 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Labarai7 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
-
Labarai7 days agoMasu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki
-
Labarai5 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
